KIWON LAFIYA: Cutar Hawan Jini, Illoli Da Matakan Kariya
- Katsina City News
- 23 Nov, 2024
- 33
Hawan jini wata cuta ce da ke addabar mutane da dama a wannan zamani, maza da mata. Ana gano wannan cuta ne ta hanyar amfani da na’urar auna jini. Idan aka auna jinin mutum ya kai kimanin 150/90 mm Hg, za a iya yanke shawarar cewa akwai yiwuwar yana fama da hawan jini. Sai dai, ana bukatar a yi akalla awo sau uku (3) a lokuta daban-daban kafin tabbatar da cewa mutum yana da wannan cuta.
Ciwon hawan jini yana iya haifar da matsaloli masu tsanani irin su ciwon zuciya, mutuwar sassan jiki, da ciwon kwada. Mutanen da ke da kiba sun fi fuskantar wannan matsala.
Rabe-Raben Hawan Jini
1. Hawan Jini Na Farko (Essential Hypertension):
Wannan nau’in hawan jini shi ne wanda ba a san dalilin da ke haddasarsa ba (Allah kadai ya sani), sai dai akwai wasu abubuwa da ake dangantawa da shi. Wadannan su ne:
- Gado (idan iyaye ko kakanni suna da hawan jini).
- Shan taba sigari.
- Rashin samun kwanciyar hankali.
- Kiba.
2. Hawan Jini Na Biyu (Secondary Hypertension):
Wannan nau’i shi ne wanda ake iya danganta dalilin faruwarsa da wasu abubuwa, kamar:
- Ciwon kansar kwada.
- Shan magungunan tsarin iyali, musamman wadanda ke dauke da sinadarin **estrogen**.
- Wasu nau’ikan cututtuka masu shafar makoko.
- Taruwar kitse a jiyoyin jini.
- Rashin samun kwanciyar hankali.
23.1 Yadda Cutar Ke Faruwa
Hawan jini yana haifar da tsukewar hanyoyin jini da kananan jijiyoyi, wanda hakan kan janyo zaizayewar hanyoyin jini da daskarewar jini. Wannan matsala tana hana isasshen jini isa wasu sassan jiki kamar kwakwalwa, zuciya, ko kwada.
Idan jini ya hau sosai har ya kai 170/90 mm Hg, zai iya haddasa fashewar jijiyoyi da ke kaiwa kwakwalwa jini, wanda zai iya janyo mutuwar sashen jiki ko duka jiki baki daya.
23.2 Alamomin Hawan Jini
1. Ciwon kai mai tsanani.
2. Jin juwa ko birgima.
3. Kasala da rashin kuzari.
4. Ciwon kirji.
5. Bugawar zuciya fiye da kima.
6. Kumburi a jiki.
7. Rashin yin fitsari yadda ya kamata.
8. Jin kara ko kuwa a kunnen mutum.
9. Rashin samun barci mai kyau.
10. Jin tsoro ko rudewa ba tare da dalili ba.
11. Ciwon kafada.
12. Kyarma ko makarkatar jiki.
Da zarar an fuskanci wadannan alamomi, yana da muhimmanci a hanzarta zuwa asibiti mafi kusa domin a tantance lafiyar jiki. Ya kamata kowane mutum da ya haura shekaru ashirin (20) ya rika zuwa asibiti lokaci-lokaci domin auna lafiyar jininsa.
23.3 Illolin Hawan Jini
1. Ciwon zuciya.
2. Mutuwar sassan jiki.
3. Makanta.
4. Hauka.
5. Kurumta.
6. Kyarma ko makarkatar jiki.
Hawan jini cuta ce mai tsanani, amma ana iya rage hadarinta ta hanyar zuwa asibiti akai-akai, kiyaye shan taba, rage kiba, da tabbatar da kwanciyar hankali. Allah ya karemu daga dukkan cututtuka.