Kiwon Lafiya: Cutar Haniya, Illolin Ta Da Hanyoyin Magance Ta
- Katsina City News
- 20 Nov, 2024
- 25
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Ciwon haniya wata matsala ce da ke shafar jikin mutum ta hanyar fitowar wani sashe na jiki ta kafar da ba ta dace ba. Wannan ciwo yana da alamomi daban-daban kuma yana bukatar kulawa ta musamman domin guje wa illolinsa. Ga bayanai dalla-dalla game da wannan matsala da hanyoyin magance ta.
Nau’o’in Dalilan Haniya
1. Rashin rufe cibiya bayan an haifi jariri.
2. Matsanancin tari wanda ke haifar da matsalar cibiya.
3. Nauyin ciki yayin daukar juna biyu wanda ke haifar da haniya.
4. Rashin ingancin wasu jijoji na jiki, musamman jiyojin cikin mutum.
5. Matsananciyar kiba da ke kara nauyi ga jiki.
Alamomin Haniya
1. Kumburi: Wani kumburi wanda baya ciwo ko zafi yayin tsaye, amma yana ɓacewa yayin kwanciya.
2. Jin Ciwo: Ciwo da ake ji sakamakon gugar da ke tsakanin abin da ya fito (haniya) da sashen jiki da ta kusanta.
3. Matsanancin Ciwon Kai: Idan haniya ta murɗe, tana iya jawo ciwon kai mai tsanani, har ma suma.
4. Zazzabi da Amai: Lokacin da ciwon ya tsananta yana haifar da zazzabi tare da amai.
Hanyoyin Magance Haniya
1. Da zarar an lura da alamomin haniya, ana shawartar zuwa asibiti mafi kusa don neman magani.
2. Kashi 90% na masu fama da haniya suna warkewa idan aka yi aikin tiyata da bayar da magunguna.
3. Kashi 10% kawai ne ke iya samun komawar ciwon bayan an yi aikin tiyata.
Hanyoyin Gane Haniya
1. Ta Alamomi: Alamomi kamar kumburi da ba shi da alaƙa da ciwo suna taimakawa wajen gane haniya.
2. Ta Hanyar Dubawa: Likita zai duba daga kan mutum har zuwa yatsun ƙafa domin tabbatar da yanayin ciwon.
Illolin Haniya Ga Jikin Mutum
1. Ƙara Aukuwa: Komawar ciwon bayan an yi aiki.
2. Fafarewar 'Yan Hanji: Matsalar ƙananan hanji.
3. Mutuwar Sashe Na Jiki: Rashin isar jini zuwa wani wuri na iya jawo mutuwar sashen jikin.
4. Cutar Kansar Jini (Leukaemia): Wata cuta mai haɗuwa da ciwon haniya.
5. Toshewar 'Yan Hanji: Rashin gudanar abinci cikin hanji.
6. Ciwon Infection: Shigar ƙananan ƙwayoyin cuta sakamakon aikin tiyata.
Ciwon haniya wata matsala ce mai warkewa idan aka kula da ita da wuri ta hanyar ganin likita da yin tiyata idan ya zama dole. Don haka, ana shawartar masu fama da irin wannan matsala su gaggauta neman magani kafin ciwon ya tsananta.
Daga Littafin Kula Da Lafiya Na Safiya Ya'u Yemal