Kiwon Lafiya
- Katsina City News
- 19 Nov, 2024
- 145
Kiwon Lafiya:
19.0 Matsanancin Ciwon Ciki
Wannan wani irin ciwo ne mai tsanani wanda kan faru ba tare da wata alamar gargadi ba. Ana buƙatar daukar matakin magani cikin gaggawa, kuma a wasu lokuta ana kaiwa ga yin tiyata don ceton rayuwa.
19.1 Yanayin Ciwon
Ciwon kan fara ne kai tsaye ba tare da bata lokaci ba. Idan ya afku, zai ci gaba har na tsawon kimanin awanni shida (6) ba tare da ya tsaya ba.
Idan ciwon ya faru sakamakon wasu ƙwayoyin cuta, za a iya ganin zazzabi mai zafi da ke kaiwa tsakanin "38°C zuwa 39°C". Idan kuma dalilin fafarewar hanji ne, mutum zai kasance yana numfashi da sauri.
19.2 Abubuwan da Ke Haddasa Wannan Ciwon
Wadannan abubuwa sun kasu gida biyu:
1. Wadanda ke kaiwa ga aikin tiyata:
- Wanzuwar ƙwayoyi a cikin ƙwada (Apendix).
- Juna biyu a wajen mahaifa wanda ke haifar da matsanancin ciwo.
- Rarakewar hanji sakamakon cutar zazzabin typhoid.
2. Wadanda ba sa kaiwa ga tiyata:
- Amai da gudawa.
- Ciwon cikin tsutsar ciki.
- Lamoniya ko cutar mafitsara.
Duk wanda ya fuskanci irin wannan matsanancin ciwo, ya kamata ya garzaya asibiti cikin gaggawa don samun magani kafin cutar ta yi muni har ta haddasa rasa rai.
20.0 Ciwon Ƙwada
Ciwon ƙwada wata cuta ce mai hana ƙwada yin aikinta yadda ya kamata. Babban aikin ƙwada shi ne tace jini da kuma fitar da wasu gurbatattun sinadarai daga jiki.
20.1 Alamomin Wannan Cuta
- Hawan jini.
- Kumburi, ciki har da kumburin ciki.
- Rashin iya yin numfashi sosai.
- Amai da tashin zuciya.
- Fitsarin jini ko na sukari.
- Kasala da rashin kuzari.
- Rashin yin fitsari ko ciwon mafitsara.
- Tari mai tsanani da tsananin zafin wurin ƙwada.
20.2 Abubuwan da Ke Haddasa Ciwon Ƙwada
- Cutar sikila.
- Ciwon sukari.
- Cutar malaria (zazzabin cizon sauro).
- Cizon kwari.
Idan an lura da ɗaya ko fiye daga cikin alamomin wannan cutar, wajibi ne mutum ya hanzarta zuwa asibiti don bincike da magani. Rashin daukar mataki cikin lokaci na iya haifar da mummunar matsala ga lafiyar mutum.
Daga littafin Safiya Ya'u Yemal na Kula da Lafiya