DANGANTAKA TSAKANIN KATSINA DA ZAZZAU.
- Katsina City News
- 19 May, 2024
- 411
Ba a samu wani cikakken bayani ba a kan Yaki tsakanin Katsina da Zazzau.
Dangantakar data fi karfi tsakanin Katsina da Zazzagawa itace ta fannin Kasuwanci da Ilimi.
Tun lokacin Sarakunan Habe, lokacin ana Kasuwancin Sahara (Transaharan Trade) Katsina ta Kasance babbar cibiyar Kasuwanci Sahara ta Kasar Hausa( Transharan Trade Centre route). Wannan daliiine yasa Katsina take hudda da Kasashe da dama wajen harkar Kasuwanci kamar Zazzau, Kano, Agades, Magrib da sauransu.
Kasar Zazzau tana daya daga cikin Kasashen da Katsina tayi huldar Kasuwanci dasu a wancan lokacin.
Lokacin da Jihadi yazo na Shehu Usman Danfodio. A Katsina Mujahidai sun Kori Sarakunan Habe a cikin shekarar 1807, inda su Haben suka gudu suka kafa Masarautar su a Maradi, a karkashin Jagorancin Dankasawa a cikin shekarar 1816. Daga nan su Haben suka kudiri aniyar kwatar mulkin su, daga hannun Fulani Dallazawa, a daliin wannan harin da Habe suke kawowa yayi sanadiyyar tashin cibiyar Kasuwanci daga Katsina zuwa Kano. Wannan ya jawo yawancin Yan Kasuwar Katsina da Malamai suka yi Hijira daga Katsina zuwa wasu sassan Kasar Hausa kamar Kano da Zazzau da sauransu. Tarihi ya nuna daliin hijirar Yan Kasuwar Katsina zuwa Kano ne yasa aka samu suna Unguwannin Galadunchi da Marna da sauransu a Kano, Wanda asalinshi mutanen Katsina ne suka kafata.
Ta bangaren Zazzau, Zuruar Sarkin Zazzau Shehu Idris sunyi Kaura daga Katsina zuwa Zazzau, wannan dalilin yasa masu Sarautar Zazzau suka kasu gida ukku (3). Akwai 1. Mallawa 2. Barebari da Kuma (3) Katsinawa. Wannan ya nuna kakannin Sarkin Zazzau Shehu Idris asalinsu Katsinawa, Wanda wannan ya Kara babbar dangantaka tsakaninmu da Zazzagawa.
(2). Ta bangaren ilimi akwai Dangantaka tsakaninmu da mutanen Zazzau. A farkon karni na 15, zuwa na 17 Katsina ta Kasance babbar cibiyar ilimin addinin musulunci a Kassr Hausa. A lokacinne Kasar Katsina ta tara manyan Malamai na addinin musulunci kamar su Danmasani, Danmarna, Dantakun, Malam Kisko Gambarawa, Malam Yahaya na Yandoto da sauransu. Almajirai suna zuwa neman ilimi daga wajensu ta bangare da dama na sassan Duniya. Mutanen Zazzau sunyi shigo Katsina neman ilimin addinin musulunci a wannan lokacin. Wannan ya Kara babbar alaka da dangantaka tsakaninmu da mutanen Zazzau.
Ta bangaren ilimin Boko. Acikin shekarar 1922, ne aka bude Katsina College, wadda ta Kasance itace ( Teacher Training College ) ta farko a Arewacin Nigeriya. Wannan dalilin yasa dalibai da dama daga bangarorin Nigeriya suka shigo Katsina domin neman ilimin Boko, misali Sardauna Sokoto Sir Ahmadu Bello yayi Karatu a Katsina, Sir Abubakar Tafawa Balewa, yayi Karatu a Katsina College, Sir Kashim Ibrahim da sauransu. A wannan lokacinne mutanen Zazzau da dama sun halarci Katsina College.
Misali, a rabon daliban Katsina College na shekarar 1935, akwai mutanen Zazia kamar guda 6 suka halar ci Katsina College. Daga cikin mutanen Zazzau wadanda suka halarci Katsina College akwai Alhaji Nuhu Bamalli, ( regional
Minister) da sauransu. Wannan ya Kara dangantaka Mai karfi tsakaninmu da Zazzagawa.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.