KADAN GADA RUKININ SARAUTUN TAFIYAR DA GIDAN MAI MARTABA SARKIN KATSINA.
- Katsina City News
- 18 May, 2024
- 638
Akwai tsarin Sarautu na Yaran Sarki, domin hidimar Gidan Sarki, Kuma akwai rawar da yake takawa. Daga cikin irin wadannan Sarautun akwai:.
1. WURO. Akwai Sarautar Sarkin Gida, baa kiransa da Sarki, Saboda ga Sarki, acikin gida, Sai a saya da Wuro.
Babban aikin Mai rike da wannan Sarautar shine, Kula da Gidan Sarki, kamar bude Gidan Sarki da rufeshi idan lokaci yayi.
2. Tambaya akan bakon da zai shigo Gidan Sarki
3. Gidan Wuro Yana daga cikin rukunin Gidan Sarki tareda iyakin shi, saboda yanayin aikin shi.
2. RUMBUNA. Wannan Sarautar ana bayar da ita ga baran Sarki Wanda aka aminta dashi. Babban aikin Runbuna shine.
1. Sarkin Hatsi.
2. Kula da duk wani Hatsi Wanda Sarki ya noma
3. Kula da Runbunan Hatsi na Sarki
Da sauransu. Malam Alin Kanta shine Runbuna na yanzu.
3. SARKIN TUWO.
Babban aikin Sarkin Tuwo, shine ya tabbatar da duk wani baran dake hidima Gidan Sarki an bashi abinci, kamar Yan Barga, da sauransu. Kulawa da dafa abincin Yan Barga da sauran masu hidimar Gidan Sarki.
4. RAGUNA.
Baya ga Sarkin Tuwo, akwai Kuma RAGUNA, Wanda babban aikin shi, shine
1. Tabbatar da lafiyar Ragon da zaa yanka ma Sarki.
2. Gasa ma Sarki nama.
3. Kulawa da RAGUNA Sarki dake cikin gida da sauransu.
Musa Gambo Kofar soro.