Ina masu cewa ba za su hada kai da wasu musulmin ba? TO, GA NAKU!
- Katsina City News
- 23 Mar, 2024
- 530
Ina masu cewa ba za su hada kai da wasu musulmin ba? TO, GA NAKU!
Yarjejeniya: Dinke baraka tsakanin mazhabobin Musulunci..
Doka ta daya:
"Musulmai al'umma ce guda daya, suna bauta wa Ubangiji daya, suna kuma karanta littafi daya, suna kuma bin Annabi daya, a kuma duk inda suke alkiblarsu daya ce, lallai Allah ya girmama su da sunan Musulunci, a wani bayani da yake a bayyane tamkar bayyanar rana, bai kamata a sauya shi da waninsa ba, bayan Allah ya zaba mana shi: (Shi ne ya sanya maku suna Musulmai), saboda haka, babu bukatar kowane irin suna, ko sifa da suka yi kutse, wadanda suke rarraba kawuna ba sa hadawa, suke kuma nesanta al'umma da juna, ba sa kusanto da su.. Banda wadanda suke karfafa da bayyana manhaji, masu karfafa ayyukan Musulunci, su ma din, da sharadin kada su zama an canza sunan Musulunci da su, ko su zama suna gasa da sunan da Allah ya kira mu da shi, kaman yada su a farfajiyar Musulunci, don su kawar da sunan da ya hade mu gaba daya, musamman abubuwan da batattun jam'iyyun da suka kaurace wa hadin-kan al'umma, da wasu 'yan tsirarun sunaye da wasu tsirarun batattu suke siffantawa".
Taron Makka 2024, a gefen dakin Allah mai alfarma, karkashin kungiyar رابطة العالم الإسلامي