TARIHIN KAFUWAR MAKABARTU NA CIKIN BIRNIN KATSINA.
- Katsina City News
- 06 Dec, 2023
- 918
Tun lokacin Sarakunan Habe wajen karni na 15 zuwa na 16 an samu bakuncin Malaman addinin Musulunci da Yan Kasuwa da sauransu anan cikin birnin Katsina wannan yayi sanadiyyar kafuwar MAKABARTU a cikin birnin Katsina daga cikin su akwai Makabartar Dantakun da Danmarna da aka kafasu tun lokacin Sarakunan Habe, akwai Makabartar Sarakunan Dallazawa wadda aka kafa Bayan Jihadi, akwai Makabartar Rimin Badawa wadda Badawa suka kafa a shekarar 1833, akwai Makabartar Sarakunan Sullubawa wadda aka kafa a shekarar 1944 da sauransu.
1. DANTAKUN.
Ita Makabartar Dantakun kamar yadda sunan ta ya nuna, Wali Dantakun shine aka Fara rufewa a wajen.
A karshen karni na 15 an samu bakuncin wani babban Malami, kuma masanin Sharia anan Katsina, Wanda ake Kira Alkhadi Muhammad ibn Ahmad Altaskati, Wanda aka fi Sani da Dantakun. Sarakunan Habe na Katsina sun nada wannan Malami a matsayin babban Alkalin Katsina. Anan ya zauna kusa da Hasumiyar Gobarau inda aka bashi gida Yana gudanar da Shariar Musulunci. Anan Katsina ya rasu aka rufeshi acikin gidan shi. Wanda daga baya wurin ne ya zama babbar Makabartar Dantakun dake Galadunci Katsina.
2. DANMARINA.
Makabartar DANMARINA ta kafu tun lokacin Sarakunan Habe. Mutum na farko da aka Fara rufewa shine Wali DANMARINA. DANMARINA babban Malami Wanda ya rayu tun lokacin Sarakunan Habe. Ya zauna a Unguwar Marina dake cikin birnin Katsina. Shima a Katsina ya rasu aka rufeshi a cikin Gidanshi. Wanda daga baya wurin ya zama babbar Makabartar Danmarna Katsina.
3. MAKABARTAR SARAKUNAN DALLAZA.
Ita wannan Makabarta ta samo asalintane tun lokacin da Amirul Katsina Malam Ummarun Dallaje ya rasu a shekarar 1836. Ance a lokacin shima acikin Gidan Korau aka rufeshi, Sai daga baya, bayan anyi wasu canje canje na Gidan Sarki Makabartar ta dawo Bayan Gidan Sarki. Days cikin Makabartar akwai Kabarin Ummarun Dallaje da sauran wasu Sarakunan Dallazawa, akwai Kuma Kabarin Galadima Dudi. A halin yanzu wannan Makabartar tana nan Unguwar Tsamiya Bayan Gidan Sarkin Katsina.
4. MAKABARTAR RIMIN BADAWA.
Makabartar Rimin Badawa kamar yadda sunan ta ya nuna, Badawa suka kafata a shekarar 1833. Badawa sunzo Katsina a lokacin Jihadin Shehu Usman Danfodio. Jagoransu Muhammad Dogo shine aka Fara rufewa a Makabartar a shekarar 1833 a cikin Gidanshi Wanda daga baya wurin ya koma babnar Makabartar Rimin Badawa.
5. MAKABARTAR SARAKUNAN SULLUBAWA.
Ita wannan Makabartar tana nan acikin Kofar soro. Asalinta Lambu ne na Sarkin Katsina Muhammadu Dikko(1906-1944. A cikin Lambu ne Sarki Dikko ya shifka Dabino yabar wasiyya cewa idan ya rasu to a kawo shi kusa da Dabinon a rufeshi, haka Kuma akayi a shekarar 1944. Shima Sarkin Katsina Sir Usman Nagoggo haka yayi ya shifka Dabino yace idan ya rasu akawo shi Nan a rufeshi. Haka shima Sarkin Katsina Alhaji Muhamad Kabir. Daga cikin Makabartar akwai Sarakunan Sullubawa da Matansu.
Idan muka duba kafuwar MAKABARTU zamu ga cewa mutanen da da Malamai da Sarakunan duk a Gidajensu ake rufesu. Saura kamar su Malam Kisko Gambarawa shima a Gidanshi aka rufeshi tun lokacin Sarakunan Habe, Kabarin Turaki Agawa dake Kusa da Gidan Sarki shima a Gidanshi aka rufeshi a shekarar 1903.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.