Rufe Bodar Nijar-Nijariya Ya Jawo Babbar Asasar Kayan Gwari A Nijeriya.
- Katsina City News
- 16 Aug, 2023
- 653
Tun bayan da aka rufe iyakokin Jijar da Nijariya, ake ta samun hasarar dimbin dukiya musamman na kayyakin masarufi na gwari kamar su Alabasa da dangoginta, tare da wasu abinci jinsin nama da suka hada da Kifi.
'Yankasuwa na ta tafka asarar kayayyakin da suka Loda trailer-traler domin shiga da su a kasar ta Nijar, inda kafin su kai ga shiga aka rufe Iyakoki wanda sakamakon haka sukai ta tafka Asara. Rahotanni daga jihar Katsina sun ce, a wannan Satin farashin Kifi ya sauka ba kadan ba, inda aka rika saida Kwalin kifi a kan naira 8,000 sakamakon karyewar farashinsa a dalilin rufe bodojin Nijar-Nijariya.
Haka abin yake a Sakkwato, inda rahotanni suka bayyana cewar Gada da ƙauyukan Gada su ma sun tafka asarorin Miliyoyin kudade inda kayan gwari irin Albasa sukai ta ru6ewa ana jefarwa a shara.
Kawowa yanzu dai 'yan kasuwa sun yi hasara mafi muni a sanadiyyar dakatar da Lodin manyan Motocin Treloli waɗanda suke ɗauke da albasa na tsawon kwanaki ba tare da sun samu ƙetaw cikin jamhuriyyar Nijar din ba, inda a ƙarshe dole motocin suka dawo gida da kayan Albasar bayan da suka yi kwanaki a tsaye ɗauke da Albasa.