Yadda hanyar Kankara zuwa Sheme ta zama siraɗin mutuwa
- Super Admin
- 12 Aug, 2023
- 525
Al’ummomin wasu garuruwa da hanyar nan da ta tashi daga Ƙankara zuwa Sheme, wadda kuma ta ratsa yankunan kananan hukumomin Ƙankara da Bakori da kuma Faskari, a jihar Katsina, ta na neman ta gagara biyuwa.
Hakan ya samo asali ne sakamakon yadda ‘yan bindiga ke yawan tare matafiya, suna yi musu fashi, da kuma sace mutane don neman kudin fansa, ko ma yi musu kisan gilla.
Wani mutumin yankin da BBC ta tattauna da shi, Umar A Umar Kakumi, ya ce ba dare ba rana ‘yan fashi suna tare mutane.
Ya ce, ‘’ An dade ana irin wannan hare-hare, don ko a ranar Jumma’ar data wuce, ranar da kasuwar Sheme ke ci, sai da ‘yan bindiga suka fito suka tare mutane har ma suka kashe wasu mutum tara tare da kora wasu 23 daji.”
‘’ Akwai jami’an tsaro don suna bin wannan hanya akai-akai, to amma duk da haka abubuwa sun yi yawa, don idan an tarba wannan hanya sai su koma waccan haka suke yi.” In ji shi.
Umar A Umar Kakumi, ya ce wannan abu yana damunsu don a yanzu ma da wuya kaga mutane sun je cin kasuwa.
Ya ce, ‘’ Babban abin da ke damunmu shi ne muhimmancin hanyar, saboda kusan duk wanda ya taso daga Nijar ko Kebbi ko Sokoto ko Zamfara idan zai je Gombe ko Bauchi ko Kano ko Katsina koma Jigawa, to wannan hanya itace mai sauki bi kuma mai sauri da za a bi hankali kwance.”
Mutumin ya ce, gashi kuma hanya ce mai kyau da gwamnati ta yi ta kana ana amfani da ita.
Ya ce, ‘’ Bay aga hanyar ce data sada jihohi, hanya ce kuma da duk manoman yankin kan yi amfani da ita wajen amfanin gonarsu kasuwa.”
Umar A Umar Kakumi, ya ce, a yanzu saboda yadda ‘yan fashin dajin suka addabi hanyar, dole mutane idan za su je jihohi kamar su Kano ko Gombe da Bauchi, koma a nan cikin jihar Katsinan, sai an yi dogon zagaye.
Ya ce, saboda muhimmancin wannan hanya suke kira ga hukumomin da abin ya shafa a kan su taimaka, duk suna iya bakin kokarinsu, suna so a kara kaimi don magance musu wannan matsala ta ‘yan fashin dajin da suke hana su bin hanyar.