Daga Wakilinmu | Katsina Times
Mazauna Rugar Bayan Dutse, wata matsugunniyar Fulani da ke kan hanyar Danguza–Kakumi a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina, sun wayi gari cikin firgici da safiyar ranar Alhamis sakamakon wani mummunan harin da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun afka wa rugar ne da asubahin fari, inda suka rika harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsoro. A yayin harin, an kashe mutum ɗaya mai suna Da’uh, wanda al’umma suka bayyana a matsayin mutum nagari kuma mai son zaman lafiya.
Baya ga kisan, maharan sun kuma kwashi dabbobi masu yawa, abin da ya jefa iyalan da abin ya shafa cikin babbar asara, la’akari da cewa yawancin mazauna yankin na dogaro da kiwon dabbobi ne wajen samun abin rayuwa.
Mazauna yankin sun shaida wa KatsinaTimes cewa lamarin ya sake tayar da hankula, kasancewar wannan ne hari na farko tun bayan cimma yarjejeniyar sulhu da aka yi a ƙaramar hukumar Bakori. Yarjejeniyar sulhun ta haifar da fatan samun zaman lafiya, inda aka ba mazauna damar komawa garuruwansu da rugoginsu ba tare da fargaba ba.
“Wannan hari ya jefa shakku akan zaman lafiyar da muka fara samu,” in ji wani mazaunin yankin, yana nuna fargabar cewa sake bullar tashin hankali na iya kawo cikas ga ƙoƙarin sulhun da ake yi.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro kan lamarin. Sai dai al’umma sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara sintiri a yankunan karkara masu rauni domin hana sake faruwar irin wannan hari.
Kisan Da’uh ya jefa al’ummar yankin cikin jimami, inda mazauna sukai fatan Fatan Allah Ya jiƙan wadanda suka rasu tare da yin addu’ar kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da rashin tsaro a Bakori da ma jihar Katsina baki ɗaya.