"Masarar da Gwamnatin jihar Katsina take rabawa Talakawa, ko Dabbobi aka bawa an ƙwaresu" Inji wani da ya samu Tallafin
- Katsina City News
- 20 Aug, 2023
- 1315
"Masarar da Gwamnatin jihar Katsina take rabawa Talakawa, ko Dabbobi aka bawa an ƙwaresu" Inji wani da ya samu Tallafin
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Al'ummar da Tallafin Masara da Gwamnatin jihar Katsina take rabawa domin rage Raɗaɗin rayuwa ya riskesu sunyi kira ga Gwamnatin jihar Katsina da ta Dakatar da Rabon Masarar kuma ta binciki 'Yan Kwangilar da suka kawo Masarar.
Wáni da Katsina Times taji ta bakinsa ya Zargi 'Yan Kwangilar da Ha'inci inda aka gurɓata Masarar da wata tsohuwar Masara maras kyau wadda ko Dabba aka bawa ita yace an kwareta.
Sana yayi kira ga Malaman Lafiya da su gaggawar Daukar Matakin hana amfani da ita ga wadanda suka samu, don kada garin neman gira ido ya tsiyaye.
"Hakika ga wanda yasan ingancin Abinci idan yaga Masarar yasan zata iya haddasa wata cutar idan aka yi amfani da ita" inji wani Masanin kiwon lafiya.
Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, haɗin gwiwa da hukumar ta jihar Katsina SEMA, ce suka bayyana fara rabon Masarar tun daga ranar 19 ga watan Agusta wanda ƙanan hukumomi 21 zasu Amfana da Tallafin Masarar.