Abin da kotun zaɓen Kaduna ta ce kan zaɓen gwamna

top-news

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kaduna ta yanke hukunci, inda lauyoyin kowanne ɓangare ke iƙirarin nasara.

Hukuncin kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Victor Oviawe, ya ce masu ƙorafin sun gaza karɓar sanarwar kafin fara shari'a (pre-hearing notice) a cikin mako ɗaya, kamar yadda sashe na 18 na kundin zaɓe ya tanada.

Haka zalika, kotun ta tabbatar da da'awar ɓangaren APC, Sanata Uba Sani cewa shaidun da Isa Ashiru ya gabatar, ba su da tushe.

Kotun ta kuma soki da'awar lauyoyin Uba Sani na cewa masu ƙorafi sun shigar da ƙara, bayan lokaci ya wuce, don haka ta yi watsi da buƙatar da suka nema.

Alƙalan kotun sun yanke hukuncin ne ranar Alhamis ta hanyar Zoom.

Wakilan ɓangarorin biyu da lauyoyinsu sun halarci zaman kotun a Kaduna, sai dai alƙalan waɗanda ba su hallara a kotun ba, sun karanta hukuncin ta majigi.

Isah Ashiru na jam’iyyar PDP ne ya shigar da ƙarar, inda ya yi zargin tafka maguɗi a zaɓensu na watan Maris.

Sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, ta fitar a watan Maris, ya nuna cewa Sanata Uba Sani na APC, ya samu ƙuri’a 730,002.

Me lauyan APC ya ce?

Lauyan jam'iyyar APC, Sanusi Musa mai lambar SAN ya shaida wa BBC cewa kotun zaɓen ta kori ƙarar da ɗan takarar PDP ya shigar.

Ya ce kotun yi watsi da buƙatar PDP ta neman a soke zaɓen, bisa hujjar cewa an yi maguɗi, amma dai kotun ta ce masu ƙorafin, ba su iya tabbatar da iƙirarin da suka yi ba.

Haka zalika, Sanusi Musa ya ce kotun ta kuma kori buƙatar ɗan takarar PDP na cewa ta tabbatar da Isah Ashiru, a matsayin wanda ya lashe zabe.

Ya ce lauyoyin APC sun soki ƙorafin PDP tun da farko na cewa, ba su shigar da ƙarar a kan lokaci ba.

A cewarsa, game da wuraren da aka soke zaɓe, kawunan alƙalan sun rabu biyu.

"Mutum biyu suka ce an soke zaɓe a akwatuna 22, kuma yawan ƙuri'un da suke wurin ya kai 16,000. Amma shugaban kotun ya ce inda aka soke zaɓen, yawan akwatunan ba su kai 22 ba, kuma yawan ƙuri'u 7,000 ne, saboda haka bai dace a ce za a taɓa sakamakon zaɓen ba."

A cewar lauyan APC, muhimmin abu dai daga ƙarshe, an kori ƙarar yanzu. "Babu ƙarar a kotu, kuma shi Sanata Uba Sani, shi ne gwamnan Kaduna."

BBC ta tambaye shi game da umarnin kotu na cewa a sake zaɓe a wasu tashoshin zaɓe. Sai Sanusi Musa ya ce "wannan ta faɗa ne. Ai ta riga ta kori ƙarar daga farko".

Ya ce ba za a sake wani zaɓe ba, sai dai fa idan jam'iyyar PDP ta ɗaukaka ƙara, kuma kotun ɗaukaka ƙara ta amince da da'awarsu, sannan ta ba da umarnin cewa sake zaɓen.

Ga bahasin lauyan PDP

Sai dai, Barista Baba Lawal Aliyu, lauyan Isa Ashiru ya shaida wa wakilin BBC da ya halarci zaman kotun cewa hukuncin da kotu ta gabatar, shi ne a je a sake zaɓe a ƙananan hukumomi guda huɗu cikin wasu mazaɓu kusan 14.

"A kotun, alƙalai ne guda uku, alƙalai biyu su ne masu rinjaye, kuma suka ce a je a sake zaɓe a ƙananan hukumomi guda hudu, shi kuma alƙali ɗaya ya ce ya tabbatar da Gwamna (Uba Sani).

Barista Baba Aminu ya ce hukunci iri biyu ne.

"Akwai hukuncin da kotun ta yi cewa sun watsar da ƙarar, saboda rashin shigar da ita a kan lokaci. Sannan kuma akwai hukuncin da ke cewa a sake zaɓe."

Ya jaddada cewa kotun, hukunci guda biyu ta bayar kuma za su ɗaukaka ƙara a kan ɓangarorin da ba su amince da su ba.

An tsaurara matakan tsaro


Tun a lokacin da aka fara sauraron ƙarar a wata uku da ya gabata an riƙa tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da ke Kaduna to amma a yanzu tsaron ya fi na baya, inda a wannan karo aka jibge jami'an tsaro a birnin fiye da a baya.

Muƙaddashin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Mansur Hassan ya faɗa wa BBC cewa an yi hakan ne domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Ya ce, rundunar ƙarƙashin kwamishinan 'yan sanda na jihar Musa Yusuf Garba ta samar da wadatattun jami'ai domin tabbatar da kare rayuka da kuma dukiyar al'umma da dukkanin masu ruwa da tsaki a shari'ar.

"Wannan ya haɗa da su kansu masu shari'a da lauyoyi da kuma duk waɗanda ke da ruwa da tsaki domin mu tabbatar da kare duk wani abu da zai zo," in ji kakakin.

Daga Shafin BBC Hausa 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *