2025: Shekara Mai cike da damuwa da ta shiga Tarihin Jihar Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes31122025_005707_FB_IMG_1767142580963.jpg



Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Katsina Times | Disamba 2025

Shekarar 2025 ta zama ɗaya daga cikin mafi munin shafuka a tarihin Jihar Katsina, sakamakon matsalar tsaro, ta’azzarar halin ƙuncin jinƙai, tashe-tashen hankalin da kuma iftila'in muhalli. Kisa da sace-sace zuwa mutuwar yara sanadin yunwa, zanga-zangar jama’a da ambaliyar ruwa da ya bannata dukiya mai yawa, shekarar ta bayyana girman ƙalubalen da ke fuskantar al’umma da hukumomi a jihar.

Wannan rahoto na musamman ya tattara manyan munanan abubuwan da suka faru a fadin Jihar Katsina daga Janairu zuwa Disamba 2025, bisa sahihan bayanai daga hukumomin tsaro, ƙungiyoyin jinƙai, da kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da na duniya masu inganci.

A tsawon shekarar 2025, ayyukan ’yan bindiga sun kasance babbar barazana ga rayuka da dukiyoyi a Jihar Katsina. Ƙananan hukumomi da dama, ciki har da Malumfashi, Kankara, Faskari, Safana, Dandume, Sabuwa da Matazu, sun sha fuskantar hare-hare, kisan gilla, sace mutane, ƙone-ƙone da kuma tilasta wa al’ummomi barin muhallansu.

Mummunan hari mafi muni ya faru ne a ranar 19 ga Agusta, 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai farmaki wani masallaci a unguwar Mantau da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi yayin sallar asuba. Sama da masu ibada da mazauna yankin 50 ne suka rasa rayukansu a harin, lamarin da ya jawo kakkausar suka da Allah-wadai daga hukumomin tsaro, shugabannin addini da ƙungiyoyin fararen hula.

Tun da fari, a watan Janairu 2025, sama da ’yan sa-kai 20 ne aka kashe a wani hari da ’yan bindiga suka kai kauyen Baure da ke Ƙaramar Hukumar Safana. Harin ya sake nuna raunin ƙungiyoyin tsaron al’umma, waɗanda galibinsu ke aiki ba tare da isassu kuma ingantattun makamai, sahihan bayanan sirri da kuma cikakken haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.

A wasu lokuta daban-daban cikin shekarar, an samu gumurzu tsakanin ’yan bindiga da jami’an tsaro, inda aka samu asarar rayuka daga bangaren fararen hula da jami’an tsaro, musamman a yankunan karkara da dazuka.

Baya ga asarar rayuka kai tsaye, tsawaita rashin tsaro ya ƙara tsananta halin jinƙai a jihar. Tsoron hare-hare ya tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu, lamarin da ya kawo cikas ga samar da abinci da hanyoyin samun abin dogaro. Haka kuma, samun kulawar lafiya ya tabarbare a wasu al’ummomin da rikici ya shafa.

A watan Yuli 2025, ƙungiyar Médecins Sans Frontières (Doctors Without Borders) ta bayyana cewa sama da yara 650 sun mutu sakamakon matsanancin tamowa a Jihar Katsina cikin watanni shida. Ƙungiyar ta danganta mutuwar da ƙarancin abinci, tsananin talauci da kuma haɗarin da rashin tsaro ya haifar. Ƙungiyoyin jinƙai sun yi gargaɗin cewa adadin na iya zama mafi yawa, domin wasu yankunan karkara ba a iya isa gare su ba.

Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu ƙungiyoyi masu rike da makamai sun kakaba haraji ba bisa ka’ida ba tare da karɓar kuɗin fansa na miliyoyin naira daga al’ummomi, tare da barazanar kai hare-haren ramuwar gayya ga waɗanda suka ƙi biya.

Fushin jama’a ya kai kololuwa a watan Nuwamba 2025, lokacin da mazauna wasu sassan Ƙaramar Hukumar Malumfashi suka gudanar da zanga-zanga kan yawaitar hare-hare da abin da suka kira gazawar gwamnati wajen daukar matakan gaggawa. Masu zanga-zangar sun rufe manyan hanyoyi tare da neman daukin tsaro cikin gaggawa.

Daga bisani, zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali bayan tsoma bakin jami’an tsaro, tare da ƙara dagula alaka tsakanin al’umma da hukumomi.

Yayin da matsalar tsaro ke ci gaba, ambaliyar ruwa ta ƙara wa al’umma wahala. A lokacin tsakiyar damina ta shekarar 2025, musamman tsakanin Yuli da Agusta, ambaliyar ruwa ta mamaye al’ummomi da dama, inda ta lalata gidaje, gonaki da muhimman kayayyakin more rayuwa. Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, hukumomin jinƙai sun tabbatar da tarwatsa al’umma da dama, musamman a yankunan karkara da ke fama da talauci da rashin tsaro tun farko.

Zuwa ƙarshen shekarar 2025, daruruwan fararen hula, jami’an tsaro, ’yan sa-kai da sauran mazauna jihar sun rasa rayukansu sakamakon tashin hankali, yunwa da matsaloli masu alaƙa da su. Mutuwar masu mutane a Masallaci, yara masu fama da tamowa da jami’an tsaro ta nuna tsananin raɗaɗin da tsawaita rashin zaman lafiya ya jawo wa Jihar Katsina.

Abubuwan da suka faru a shekarar sun nuna rauni a tsarin tsaron jihar, tsarin samar da abinci da kuma haɗin kan al’umma. Duk da ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke ci gaba da yi, girman matsalolin ya nuna buƙatar gaggawar samar da tsare-tsaren tsaro masu ɗorewa, faɗaɗa ayyukan jinƙai da kuma hanyoyin warware rikice-rikice da al’umma za su taka rawa a ciki.

Yayin da Jihar Katsina ke duban shekarar 2026, darussan 2025 sun fito fili. Dole ne masu ruwa da tsaki su wuce maganganu zuwa aiki mai ma’ana domin dawo da tsaro, kare rayuka da dukiya da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa da jama’a za su ji a rayuwarsu ta yau da kullum, ba wai a takarda ba ko bayyana tsaro a baki, a zahiri ana ganin sabanin haka.

Follow Us