Babangida Albaba, ya zama shugaban Majalisar Kwalejojin Kimiyya da fasaha na Najeriya
- Katsina City News
- 27 Sep, 2023
- 1039
An nada Dr. Babangida Abubakar Albaba a matsayin shugaban majalisar shugabannin kwalejojin kimiyya da fasaha na kasa "COHEADS" wanda kuma shi ne shugaban makarantar cibiyar fasaha da gudanarwa ta katsina.
Nadin ya biyo bayan wa'adin tsohon shugaban Dr. Usman M. kallamu wanda kuma shi ne shugaban kwalejin kimiyya ta tarayya dake damaturu a Ranar 07/08/2023
Sanarwar ta fita ne bayan kammala zama na majalisar kungiyar "COHEADS" karo na dari da hamsin da biyu 152 a ranar laraba 27/09/2023,
mambobin majalisar ta "COHEADS" sun yanke shawarar nada Dr. Babangida Abubakar Albaba shugaban makarantar cibiyar fasaha da gudanarwa ta jihar katsina a matsayin sabon shugaba.
Nadin kuma ya fara nan ta ke. Yayin da majalissar kungiyar "COHEADS" ta amince da hakan tare da yi mashi murnar zama sabon shugaban.