Daga Ibrahim Musa Kallah
Shugaban Karamar Hukumar Mani, Dr. Yunusa Muhammad Sani Bagiwa, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin cikakken tsarin ci gaban Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, domin hanzarta ci gaba da inganta walwalar al’umma a fadin yankin.
Dr. Bagiwa ya bayyana hakan ne yayin wani zagayen duba ayyuka da ake aiwatarwa, inda ya jaddada cewa gwamnatin karamar hukumar na mayar da hankali kan kawo ingantaccen ci gaba ta hanyar zuba jari a bangarori daban-daban kamar ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa, noma da bunkasa matasa.
Ya ce dukkan ayyukan da karamar hukumar ke aiwatarwa suna da nasaba kai tsaye da tsarin ci gaban Gwamna Radda, yana mai tabbatar da cewa jama’ar Mani za su ci gaba da amfana daga nagartacciyar shugabanci da gaskiya wajen gudanar da mulki.
Ilimi
Karamar hukumar ta gyara tare da inganta makarantu da dama na firamare da sakandare, ta inganta ajujuwa da kayan koyarwa, tare da karfafa bangaren malamai domin habaka ingancin ilimi musamman a karkara
Kiwon Lafiya
An gina sabuwar cibiyar lafiya domin fadada damar samun kula da lafiyar jama’a. Haka kuma an sabunta wasu cibiyoyin lafiya da dama tare da tura karin ma’aikatan lafiya zuwa yankunan da ke da karancin ma’aikata.
Samar da Ruwa
Domin magance matsalar karancin ruwa, an gyara da kuma saka sabbin ruwan burtsatse (boreholes) da sauran tsarin samar da ruwa a kauyuka daban-daban, wanda hakan ya inganta samun ruwan sha mai tsafta.
Noma
Manoma a fadin karamar hukumar sun amfana da takin zamani, iri ingantattu, injinan ban ruwa, taraktoci da sauran kayan aikin gona domin karfafa noman gargajiya da na zamani, tare da inganta rayuwar jama’a.
Bunkasa Matasa
Gwamnati ta kirkiri shirye-shiryen horaswa da tallafi ga matasa, ciki har da bunkasa sana’o’i, kayan aiki, da tallafin karatu domin rage zaman banza da karfafa dogaro da kai.
Dr. Bagiwa ya yaba da karin ‘yancin da ake bai wa kananan hukumomi, yana mai cewa hakan ya ba su damar gudanar da ayyuka cikin sauri da inganci wanda ke kaiwa ga amfanin kai tsaye ga al’umma.
Ya tabbatar wa jama'a cewa a watannin da ke tafe za a kaddamar da karin muhimman ayyukan ci gaba, yana mai jaddada cewa Karamar Hukumar Mani za ta ci gaba da zama abin koyi wajen shugabanci na gari da ci gaban kasa.
Dr. Bagiwa ya yi kira ga jama’ar Mani da su ci gaba da bada hadin kai, yana mai cewa Gwamna Radda na shirin kawo karin manyan ayyuka da za su ci gaba da sauya fasalin jihar tare da inganta rayuwar al’umma domin tabbatar da amfanin dimokuradiyya.
Karshe.