Radda Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Gwiwar Duniya da Sabon Tsarin Ci Gaban Katsina a Taron Zuba Jari na 2025

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24112025_150532_FB_IMG_1763996653808.jpg

KatsinaTimes | 24 Nov 2025

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen waje, sabunta tsare-tsaren ci gaba, da daidaita dukkan ayyukan bunƙasa jihar su ne ginshiƙan manufofin gwamnatinsa na canza tsarin tattalin arzikin jihar. Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin zaman tattaunawa a Katsina Economic and Investment Summit 2025, da aka gudanarwa daga ranar 24 zuwa 25 ga watan Nuwamba, dakin taro na Continental Support & Events Center, Katsina.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta kafa Katsina State Development Management Board (KSDMB) domin zama cibiyar da za ta tattara, lura, da jagorantar dukkan dangantaka da abokan ci gaba a matakai na ƙasa da na ƙasa da ƙasa. A cewarsa, manufar hukumar ita ce “saka idanu, gina haɗin gwiwa, inganta dangantaka a duk matakai, da kuma daidaita dukkan ayyukan ci gaba a dandamali guda domin samun sauƙin sa ido da haske.”

Ya jaddada cewa Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka fi bayyana kwazonsu a shirye-shiryen da Bankin Duniya ke tallafawa, musamman shirin AGILE, inda jihar ke cikin manyan masu yin fice a fadin ƙasa. Radda ya kuma yi nuni da tallafin da aka bai wa mutanen da suka rasa muhallansu (IDPs) a Jibia ƙarƙashin shirin UNDP tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa jihar ta faɗaɗa shirin Nigeria for Women Project daga kananan hukumomi uku na farko zuwa dukkan 34 na jihar, bayan gwamnatin ta saka ƙarin Naira biliyan 4 a matsayin kudin haɗin gwiwa domin tallafa wa mata musamman a yankunan karkara.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta kulla muhimman haɗin gwiwa da ƙungiyoyi daban-daban daga Amurka. Ciki har da yarjejeniya da World Relief Agency, Michigan, wadda ta ba da kwantena 10 na kayan lafiya masu darajar Dala miliyan 10, da kuma haɗin gwiwa da Pure Life Medical Equipment, wadda ita ma ta aika da wasu kwantena 10. Har ila yau, wata ƙungiya daga Amurka ta ba da kwantena 10 na kayayyakin ilimi, inda biyu daga ciki suka iso jihar tuni.

Dangane da bunƙasa wutar lantarki, Radda ya tabbatar da cewa ana kan gina tsarin samar da wutar mai amfani da Ruwa mai ƙarfin megawatt ɗaya a Danja ta hanyar sabon haɗin gwiwa da ƙwararru.

A makon da ya gabata, Jihar Katsina ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Hukumar Tsaron Iyakoki ta ƙasar Belarus, domin ƙarfafa tsaro da inganta dabarun yaki da matsalolin zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa waɗannan shirye-shirye na cikin tsare-tsaren da aka tsara domin mayar da Jihar Katsina cikin jihohin da ke da ƙarfi wajen zuba jari da yin gogayya da sauran jihohin ƙasar. Ya tunatar cewa Katsina ta dade tana da tarihin ilimi da manyan mutanen da ta samar a fannoni daban-daban.

“Mun buɗe ƙofofin haɗin gwiwa da dama a duniya domin tabbatar da cewa Jihar Katsina na da matsayi da zata iya yin gogayya da kowace jiha a Najeriya,” in ji shi.

Follow Us