Daga Wakilin Mu | Katsina Times
Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), reshen Jihar Katsina, ta gudanar da wata walima tare da bikin karramawa ga tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya bayan shekaru suna hidima cikin kwarewa da gaskiya. An gudanar da taron ne a ranar Asabar, 15 ga Nuwamba, 2025, a dakin taro na Katsina State Institute of Technology and Management (KSITM), inda manyan jami’ai, ma’aikata, iyalan wadanda aka karrama da sauran baƙi suka halarta.
Taron, wanda wasu suka bayyana a matsayin na tarihi, ya kasance domin tunawa da gudunmawar tsofaffin ma’aikata da suka gina tubalin gudanar da ayyukan hukumar, musamman wajen kididdiga, gudanar da ayyukan ƙidaya, da tsarin gudanarwa na yau da kullum.
A jawabinsa na bude taron, Daraktan Gudanarwa na Hukumar, Malam Usman Sa’idu, ya ce NPC na da nauyin tunawa da ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen sauke nauyin ayyukan gwamnati. Ya ce irin wannan girmamawa na kara inganta aiki, yana kuma zuga ma’aikatan da ke kan aiki su kara dagewa wajen gudanar da aikinsu da adalci.
Ya kara da cewa da dama daga cikin wadanda aka karrama sun taka muhimmiyar rawa a manyan ayyukan ƙidaya na kasa, nazarin halin jama’a, wayar da kan al’umma, da kuma inganta tsarin gudanarwa na hukumar a jihar.
“Wannan taro ba wai na karrama mutane kadai ba ne, har ma da tunawa da irin gudunmawar da suka bayar wajen gina wannan hukuma,” in ji shi. “Sun bar mana abin koyi, kuma wannan girmamawa tunasarwa ce ga dukkan ma’aikatan gwamnati kan muhimmancin gaskiya da jajircewa.”
Wasu daga cikin wadanda aka karrama sun hada da: Alhaji Adamu Tafida, Alhaji Ishaq Lawal, Malam Sale Lawal, Alhaji Sa’idu Usman Waziri, Alhaji Bala Idris Mai Ruwa, Hajiya Rabi Sallau Bala Riba, Alhaji Sani Muhammad Kura, Hajiya Fatima Bashir Kaita, Alhaji Sani Haruna
Da Malam Lawal Ahmad Abubakar Mai’adua
Wasu daga cikin wadanda aka karrama sun yi jawaban godiya, inda suka nuna farin cikinsu bisa wannan daukaka da aka yi musu. Sun gode wa hukumar bisa tunawa da su bayan ritaya, tare da yi wa sabbin ma’aikata nasiha kan su dage da aiki cikin gaskiya, kwarewa da nutsuwa.
Haka kuma, sun yi addu’a ga Allah ya ba da sauki da samun ikon kammala aiki ga wadanda har yanzu suke aiki a hukumar.
Taron ya samu karin armashi ta hanyar gabatar da bayanai kan tarihin ayyukan hukumar, nuna gogewar tsofaffin ma’aikata.
A karshe, hukumar NPC ta jaddada cewa za ta ci gaba da rubuta tarihin gudunmawar tsofaffin ma’aikata domin su kasance abin koyi ga sabbin ma’aikata masu tasowa. An rufe taron da mika takardun yabo, kyaututtuka da hotunan tunawa ga wadanda aka karrama, kana aka ci abinci tare cikin nishadi.