Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Jihar Katsina ta samu labarin wata jita-jita da ake yadawa cewa magoya bayan Katsina United sun nuna halin rashin da’a tare da jikkata wani a lokacin wasan da aka buga tsakaninsu da Barau FC, wanda ya tashi 1–1.
Bayan cikakken bincike da tabbatarwa daga jami’an wasan, hukumomin tsaro, da masu sa ido masu zaman kansu da suka kasance a filin wasa, Ma’aikatar na mai ƙaryata wannan jita-jita gaba ɗaya, domin ba ta da tushe kuma ƙarya ce kawai.
Dukkan rahotanni sun tabbatar da cewa wasan ya gudana cikin kwanciyar hankali. Masu kallo sun nuna halin kirki, kuma ba a samu wani abin tashin hankali ko jikkata wani mutum ba tun kafin wasa, a lokacin wasan, ko bayan an gama. Magoya baya daga ɓangarorin biyu sun nuna ƙarfin hali da girmama juna.
Ma’aikatar na yabawa al’ummar Jihar Katsina, musamman magoya bayan Katsina United, bisa kyakkyawan halayensu da jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya. Katsina ta dade tana da suna wajen nuna ladabi da biyayya a dukkan harkokin wasanni, kuma wannan wasa ya sake tabbatar da hakan.
Ana shawartar jama’a da su rika tantance bayanai kafin yada su, tare da nisantar watsa jita-jita marasa tabbas da ka iya tayar da hankalin jama’a ba tare da dalili ba.
Ma’aikatar na nan a shirye wajen ci gaba da tabbatar da ingantattun harkokin wasanni masu cike da kwanciyar hankali da kare lafiya ga dukkan magoya baya.