Daga Abu Shadrach, Abuja
Dukkan tsoffin shugabannin jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) daga jihohi 36 na Najeriya da Babban Birnin Tarayya (FCT) sun hadu tare da sake jaddada cikakken goyon bayansu ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu (PBAT).
A cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, tsoffin shugabannin CPC sun kada kuri’ar amincewa da shugabancin Shugaba Tinubu, inda suka yaba da irin jagorancinsa da kuma kokarinsa na ci gaba da gyara Najeriya domin samun ci gaba da kwanciyar hankali.
Taron ya kuma jaddada muhimmancin hadin kan kasa, inda aka yi kira ga ’yan Najeriya da su guji duk wani yunkuri ko tasirin waje da ke neman raba kan al’umma ko tada rikici a cikin kasa.
Manyan shugabanni irin su Sanata Tanko Al-Makura da Rt. Hon. Aminu Bello Masari sun yi jawabi a wajen taron, inda suka yabawa jajircewar tsoffin shugabannin CPC tare da yin kira ga ’yan kasa masu kishin Najeriya da su ci gaba da marawa gwamnatin nan baya wajen ganin an cimma burin gina kasa mai karfi da arziki.