Muna miƙa godiya da jinjina ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, bisa irin hangen nesansa da jajircewarsa wajen zaɓen ƙwararre, jajirtacce, kuma nagartaccen ɗan siyasa kamar Engr. Surajo Yazid Abukur a matsayin Danmajallisar Zartarwa. Wannan zabin ya tabbatar da cewa Gwamna Radda na da cikakken ƙwarewa wajen tantance mutanen da ke da cancanta da kishin ƙasa.
A cikin shekaru shida da Engr. Surajo Yazid Abukur ya jagoranci KASROMA, an shaida irin gagarumar nasara a fannoni da dama. Ya zamo mutum mai kishin ci gaban jihar Katsina, wanda ya sadaukar da lokaci da ƙwarewa wajen inganta hanyoyi da magudanan ruwa a duk faɗin jihar. A karkashinsa, KASROMA ta zama cibiyar da ke tabbatar da gyaran hanyoyi, sabunta tituna, da sauƙaƙe zirga-zirga tsakanin al’umma.
Baya ga haka, Engr. Surajo Yazid Abukur Ph.D FNSE ya taka rawa mai muhimmanci a siyasar jihar Katsina, musamman a lokacin yaƙin neman zaɓe na jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Ya kasance cikin tawagar da suka zagaya mazabun kananan hukumomi gaba ɗaya tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar domin tabbatar da nasarar APC. Goyon bayansa ga jam’iyyar ba kawai na baki ba ne, ya kasance na aiki, na sadaukarwa, da gaskiya.
Wani abin alfahari kuma shi ne, Engr. Surajo Yazid Abukur shi ne mutumin farko da ya fara zama Kwamishina daga karamar hukumar Rimi tun lokacin da aka kirkiro ta. Wannan tarihi yana nuna cewa tun farko yana daga cikin mutanen da suka kafa siyasa mai inganci a yankin Rimi da Katsina gaba ɗaya.
Engr. Surajo Yazid Abukur mutum ne mai hakuri, natsuwa, da jajircewa wajen gudanar da al’amuransa. A matsayinsa na ɗan siyasa da injiniya mai hangen nesa, ya kasance yana taimaka wa al’umma ta fannoni daban-daban ta hanyar tallafawa matasa, samar da ayyukan yi, da kuma ƙarfafa masu ƙananan sana’o’i. A kullum yana ganin cewa ci gaban siyasa ba zai yiwu ba sai an ba matasa dama su taka rawa.
A yau, muna taya shi murna da fatan alheri bisa irin wannan gagarumar gudunmawa da yake bayarwa, ba kawai ga gwamnati ba, har ma ga jama’a baki ɗaya. Allah ya ƙara masa ikon ci gaba da yin abin kirki, ya kuma ba shi lafiya da ɗorewar nasara a duk inda ya tsinci kansa.
Muna sake jinjina da godiya ga Gwamna Dikko Umaru Radda bisa wannan kyakkyawan tunani na bai wa Engr. Surajo Yazid Abukur wannan matsayi mai muhimmanci, wanda ya dace da irin kwarewarsa da nagartarsa.
Allah ya taimaki Jihar Katsina. Allah ya taimaki jam’iyyar APC. Allah ya taimaki Nigeria baki ɗaya.
Gamayyar Ƙungiyoyin Magoya Bayan Jam'iyyar APC