Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon gwamnan jahar Kano, kuma shahararren ɗan siyasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa a yau, 21 ga Oktoba, 2025.
Shugaban ya taya ƴan uwa da abokan arzikin Kwankwaso da ma tawagar siyasarsa murna a yayin da suke bikin wannan rana mai muhimmanci.
Shugaban ya ce duba da irin gagarumar gudummawa da Kwankwaso ya baiwa ƙasar nan a dukkan mukaman shugabanci daban-daban da ya rike, kama daga matsayinsa na tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a Jamhuriya ta Uku da aka dakatar, sannan Gwamnan Jihar Kano na wa’adi biyu, kana Ministan Tsaro, da kuma Sanata mai wakiltar Yankin Kano ta Tsakiya, Kwankwaso ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban kasa.
Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa ķarin haɓakar tasirin Sanatan a Arewacin Najeriya, musamman a Jihar Kano, na da nasava da irin salon siyasarsa da ke bai wa muradun al’umma fifiko, wanda tayi kama da salon siyasar marigayi Mallam Aminu Kano da marigayi Alhaji Abubakar Rimi.
"Sanata Kwankwaso yana nan a matsayin aboki kuma takwaran aikina tun muna yan majalisar tarayya a 1992 sannan a matsayin gwamnoni a 1999"
"Har ila yau, mun yi aiki tare a yayin gwagwarmayar kafa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Duk da cewa daga baya ya bar APC don kafa tasa Jam’iyyar ta New Nigeria Peoples Party (NNPP), amma abu mafi muhimmanci shine kasancewarsa jagora a sahun gaba a bangaren siyasa,”
Shugaban ya yi wa Kwankwaso fatan alheri, ɗorewar lafiya, da kuma karin shekaru masu amfani cikin hidimar al’umma.