Dan katsina ya ciri Tuta; Alhaji Murtala Safana ya zama "ICON' Na Nigerian institution of surveyors.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17102025_083016_IMG-20251017-WA0017.jpg

@ katsina Times.



 A karon farko a tarihin kafuwar Nigerian institution of surveyors ta ba wasu membobin ta mutane biyu lambar girmamawa mafi girma mai suna "icon of Nigeria institution of surveyors' 
Daya daga cikin mutanen biyu shine Alhaji Murtala safana FHIS.Barde kerarriya a masarautar katsina.
Anyi wannan taron karramawar a dakin taron na tunawa da Marigayi shehu musa yar adua dake Abuja, a ranar Alhamis 16 ga watan satumba. 
An bada lambar yabon ne ga Alhaji Murtala safana a taron  NIS karo na 43 wanda aka hada da  lacca akan halin da kasar Najeriya ke ciki,wanda aka gayyaci sanan ne masanin tattalin arzikin nan na Najeriya Mista Pat Utomi.
A taron wanda masana harka surveyors na kasa suka taru an jinjina da yabon murtala safana akan irin gudummuwar da yake ba kungiyoyin cigaba a fadin kasar nan.

"Yan uwa da abokan arziki sun sa albarka wanda suka jinjina da  yabo da irin halayyar Murtala safana  abin koyi da kyawawan misali.
Murtala safana  yana da daya daga cikin gwarazan "yan katsina da suka kawo ma kasar nan cigaba ta inda yayi aiki a Abuja.
Yana kuma daya daga cikin "yan katsina gwaraza masu kishin katsina wadanda suka dade suna taimakon dai dai ku da kungiyoyi matasa da cigaba a jahar katsina. 
Yana cikin wadanda suka taka rawa wajen nasarar cin zaben Malam umaru musa "yar adua a shekarar 1999.wanda mulkin Marigayi umaru shine asasin tubalin Gina sabuwar katsina. 
Jigo ne a cigaban masarautar katsina.Murtala safana.Badallaje ne, wanda yake ya fito daga gidan sarautar sarkin Musulmi Umarun Dallaje.
Safana masu aikin alheri  ne wanda basu son a fada kuma basu fadi, irin su kadan ne a jahar katsina.

Follow Us