Binciken musamman: Hukumar KASSAROTA na cikin Hayaniya
...Zargen-zargen Almundahanar kuɗi.
Daga jaridun Katsina Times
A ranar 11 ga watan Satumba, 2025 Hukumar 'Public complaints and anti corruption commission Katsina State' (Hukumar karɓar koken jama'a da hana cin hanci da rashawa) suka aika da wata wasiƙa ga Darakta-Janar na KASSAROTA, suna neman ya yi masu bayanin yadda ya sarrafa wasu kuɗaɗen Hukumar ba tare da bin ka'idojin kashe kuɗi ba kamar yadda gwamnati ta tanada.
Takardar mai shafuka shida, wadda editocin jaridun Katsina Times suka tabbatar da ingancinta, ta kawo duk yadda aka sarrafa wasu kuɗaɗen Hukumar ba tare da bin ka'ida ba, har da kawo asusun ajiyar banki wanda aka yi amfani da shi wajen karya dokokin da suke ikirarin an yi.
Kamar yadda takardun da jaridun Katsina Times suka gani, suka nuna, Darakta-janar na KASSAROTA, ya rika amfani da asusun ajiyar Bankin sa yana wasu ayyukan na KASSAROTA.
Takardar ta Katsina Anti corruption ta karkare da cewa, abin da Darakta-Janar din ya aikata sun saɓa ka'idoji kamar haka: Saba ka'idojin tafiyar da kuɗin gwamnati a hukumance.rashin bin kaidar kashe kudi na ofis, kamar yin takardar bukatar kashe kudin da kuma botsa kafin a fitar da kudaden. Rashin ingantaccen bayanin duk kuɗin da aka kashe. Zargi da alamar kamar ana son aikata rashin gaskiya.
Bayan Hukumar Anti corruption ta jahar Katsina ta aika da wasiƙarta, kafin KASROTA ta ba da amsa, sai kwamitin amintattu da gwamnatin Katsina ta kafa ma KASSAROTA suka kira taro.
A taron sun titsiye Darakta-Janar ɗin da ya yi masu bayanin me ke faruwa a Hukumar?
Majiyoyi a zaman sun ce, an yi zaman ba daɗi. Kuma an yi masu bayanin da suka ce sam ba su gamsu ba. Sun ɗauki bayanan da aka yi masu a rubuce aka rufe taro da addu'a.
A wata wasiƙar da jaridun Katsina Times suka samu, wanda kuma suka tabbatar da ingancinta.
KASSAROTA sun aika da amsar takardar da aka rubuta masu a ranar 23 ga Satumban 2023, wasiƙar mai shafi uku, Darakta-janar na KASSAROTA ya yi ƙoƙarin ba da amsa ga duk zargen-zargen da ake masa.
Amsar da ya ba da da tuhumar da aka yi masa yana jiran sakamakon da Anti corruption commission ta jihar Katsina za ta fitar da matsayar ta.
Jaridun Katsina Times sun gano akwai zargin wasu bococin da aka yi su bayan an aika da takardar binciken. Sannan akwai wasu kuɗaɗen Naira miliyan 23 da aka amince a yi aiki da su, amma kuma milyan 33 aka fitar.
Duk wannan bambancin da ke ga amsar da aka bayar. Hukumar ta Anti corruption ce za ta tantance ta dauki matsaya da gano gaskiya.
Jaridun Katsina Times sun tuntuɓi Sakataren na Anti corruption na jihar wanda ya tabbatar mana da cewa, Darakta-Janar na Hukumar ta KASSAROTA ya ba su amsar takardar, su kuma suna aiki a kanta.
Ya ce, har yanzu suna kan bincike bisa amsar da ya bayar.
Ana tsakar jiran sakamakon binciken Anti corruption na Katsina, sai kuma ga gayyata daga Majalisar dokokin jihar Katsina.
Majiyoyi daban-daban a Majalisar sun ce duk maganar ɗaya ce.
Tambayar da aka yi ma Darakta-janar na KASSAROTA ita ce, me ke faruwa a KASSAROTA?
An tabbatar wa jaridun cewa, Daraktan ya ba da amsar da shugabannin Majalisar suka ƙarƙare da cewa, su bar maganar a jira sakamakon binciken Anti corruption na jihar Katsina.
Duk ƙoƙarin jin ta bakin KASSAROTA ya ci tura. Wani da bai son a ambaci sunansa ya ce, tunda lamarin na gaban Hukumar bincike, ba wanda zai ce komai, sai an kammala.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook; katsina city news. Social media handles. Katsina times. 07043777779