KASSAROTA Ta Karɓi Sakamakon Shawarwarin Kungiyoyin Sufuri Kan Matsalar Lodin Wuce Kima.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08102025_153445_FB_IMG_1759937660999.jpg



Auwal Isah | Katsina Times  

Hukumar kula da tsaro da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Katsina (KASSAROTA) ta karɓi daftarin sakamakon shawarwarin shugabannin kungiyoyin sufuri na fadin jihar kan matsalolin lodin wuce kima da kuma haɗa dabbobi da mutane a mota ɗaya zuwa wasu sassan Nijeriya.

Karɓar shawarwarin dai ya biyo bayan wani zama da hukumar ta KASSAROTA ta yi a kwanakin baya tare da masu ruwa da tsakin kan Tsaro da Sufuri, inda ta jagoranci kafa wani kwamitin masu ruwa da tsaki bisa umarnin gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda, sakamakon korafe-korafen da wasu kungiyoyi suka aika wa gwamnan kan matsalar lodin wuce kima da kuma haɗa dabbobi da mutane cikin mota ɗaya zuwa wasu jihohin kudancin kasar.

A yayin karɓar sakamakon shawarwarin a ranar Laraba, Daraktan KASSAROTA, Manjo Yahaya Garba Rimi (mai ritaya), ya bayyana cewar daftarin shawarwarin da shugabannin kungiyoyin sufuri suka kawo, za a hada su da wanda su ma hukumomi a nasu bangare suka bayar, a yi masa bita, sannan a hada kacokam a hannanta shi gwamnan don daukar mataki, wanda su kuma a matsayinsu na hukumomin kula da dukiya da rayukan al'umma za su aiwatar.

 “Alhamdulillah, kungiyoyin nan sun sanar da mu cewa sun yi nasu zauna, kuma sun zo da sakamakonsu. Mu ma tare da jami’an tsaro mun zauna, za mu haɗa dukkan shawarwarin nan mu duba su kafin mu tura wa gwamnati, domin ita ta yanke hukunci da kuma bayar da umarnin abin da za a aiwatar.” In ji shi.

A nasa jawabin, Shugaban NURTW na Jihar Katsina, Alhaji Musa Garba, wanda ya wakilci sauran shugabannin kungiyoyin sufuri a mika sakamakon, ya bayyana cewar shawarwarin da suka samar za su taimaka sosai wajen kawo ƙarshen matsalolin musamman ta lodin wuce kima.

Ya ce: “Tuni mun ɗauki matakai a ƙungiyoyinmu domin ladabtar da duk wani direba da aka kama yana yin lodin wuce kima," yana mai bayyana cewa matakin kuwa na iya kaiwa ga tara ko dakatar da direba.

Ya kuma jinjinawa hukamar ta gwamnati da hukumar KASSAROTA kan wannan yunkuri da aka zo da shi don kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma, "Da ma gwamnati ba za ta zuba idanu tana kallon ana ana wasa da dukiya da rayukan rayukan al’umma ba,” yana mai cewar duk matakin da aka dauka kan wanna matasala ya yi daidai.

Ya ƙara da cewa kungiyoyin sufuri za su ci gaba da wayar da kai da kuma gargadin direbobi da fasinjoji game da illolin da lodin wuce kima ke tattare da shi, inda ya roƙi jama’a da su rika sanar da su da zarar sun ga wani direba yana aikata hakan.

Duk a wajen zaman karbar rahoton, shugabannin kungiyoyin sufuri, jami’an tsaro da sauran membobin kwamitin sun yi cikakkiyar bitar rahoton sakamakon shawarwarin, inda aka tattara su tare da na KASSAROTA da jami’an tsaro domin sake bitar su a zama na gaba, kafin a kammala daftarinsu a miƙa sakamakon ƙarshe ga Gwamnan domin ɗaukar mataki.

Follow Us