Daga Al-Amin Isa
Zamani yazo, Allah yakawo mu lokacin da wasu malaman mu na addini sun zama content creators. Suna amfani da addini wurin yin content domin buƙatun su, ko na wasu mahukunta. Wasu malaman abin nasu neman suna ne bawai tsabar ilmi ne dasu ba, kuma suna son a san da zaman su, amma sunan su ba zai kai lungu da saƙo tsakanin musulmi ba domin basu da ilmin da zasu kwarorowa jama’a yadda jama’a zasuyi na’am dasu. Sabida haka sai su fara tattauna wasu mas’aloli da basuda wani amfanin tattaunasu sai don kawai dama content ne don su tada yamutsi da muhawara tsakanin jama’ar musulmi ta haka sunansu zai fito. Wasu kuma mahukunta ke amfani dasu domin su tada wani yamutsi yadda za’a kauda hankalin jama’a daga wasu matsaloli a juya hankalinsu zuwa tattauna abinda bashida wata fa’ida ta kowacce fuska zaka kalli mas’alar.
Akwai mas’aloli dayawa da suka dami jama’ar musulmin Najeriya yanzun. Yana da kyau idan da malamai zasu mayar da hankali wurin bamu ilmi da zai ƙara sanya tsoron Allah cikin zukatanmu da kuma yadda zamu sabunta imanin mu koda yaushe.
Amma Malamai suzo suna magana kan abinda bashi da wata fa’ida illa banda jawo rarrabuwar kawuna tsakanin musulmi sabida suna neman suna ta hanyar ko da yaushe sunan su ne kawai suke so jama’ar musulmi su rinƙa yawo dashi ana tattaunawa akan wata mas’ala da suka ɗauko wadda kuma bata cikin abinda ke gyara ma mutum addinin sa sai dai ma ɓata tsakaninmu.
Misali lada nawa za’a baka don kasan yadda Annabi yazo duniya? da aski yazo? Da kugunu yazo? Idon shida da kwalli ko babu a lokacin da aka haifeshi? Shin sanin makomar iyayen Annabi na daga cikin abinda za’a yimuna hisabi kanshi ranar ƙiyama? Balle yazama dole sai mun tattauna ita wannan mas’alar? Lada nawa za’a rubuta maka idan kasani? Miye kuma girman zunubin ka idan baka sani ba?
Malamai fa su daina raina muna wayo mun san content creators cikin su yanzun. Idan kana son ka rinƙa creating content ɗinka to ka rinƙa yimuna wanda zai gyara muna alwala, sallah, tsarki da yadda zamu mu’amalan ci jama’a musulmi da wanda ba musulmi ba. Ku rinƙa yi muna content na yadda zamu tarbiyantar da iyalanmu.
Idan ba hakaba mu dai sai muce muku Allah ya isa da kuke jawo muna matsalolin da ke kawo muna rarrabuwar kawuna maimakon ku haɗa kanmu.