Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times Political Desk
Sabon rikici ya sake kunno kai a jam’iyyar PDP bayan manyan shugabannin biyu, Shugaban rikon kwarya, Ambasada Umar Ilya Damagum, da Sakataren Kasa, Sanata Samuel Anyanwu, suka aikawa hukumar INEC wasiku masu dauke da sabanin umarni kan gudanar da tarukan zaben shugabanni na jihohi.
A wata wasika mai kwanan wata 25 ga Satumba, 2025, Shugaban PDP, Ambasada Damagum, ya sanar da INEC cewa an jinkirta tarukan jihohin Cross River, Plateau da Kebbi.
Ya bayyana “dalilan da ba a zata ba da kuma matsalolin shirya taron” a matsayin dalilin jinkirin. Sai dai ya tabbatar da cewa sauran jihohi tara za su ci gaba da taruka kamar yadda aka tsara, sannan daga baya za a fitar da sabbin ranaku ga jihohin da abin ya shafa. Damagum ya kara da cewa wasikar tasa na nufin sanarwa ne kawai ga INEC ba sanarwar shirin taro ba, kamar yadda Sashe na 82(1) na Dokar Zabe ta 2022 ya tanada.
A wata wasikar kuma da sakataren jam'iyar na ƙasa ya aika a ranar 26 ga Satumba, 2025, Sanata Anyanwu, ya rubuta wata sabuwar wasika ga INEC inda ya soke umarnin Shugaban jam’iyyar kai tsaye.
Ya dage cewa tarukan a jihohin Cross River, Plateau da Kebbi za su “gudana kamar yadda aka tsara tun farko”, yana mai umartar INEC da ta yi watsi da wasikar Shugaban. Har ila yau, ya bayyana cewa umarnin shi ne kadai ya kamata hukumar ta yi aiki da shi, abin da ke nuna kalubalantar ikon Shugaban jam’iyyar.
Sabani tsakanin manyan jami’an ya sake tayar da fargabar rarrabuwar kawuna a PDP, daidai lokacin da jam’iyyar ke shirye-shiryen tarukan jihohi a kan tunkarar zaben 2027.
Hukumar INEC ba ta fitar da sanarwa kan batun ba. Sai dai majiyoyi daga cikin hukumar sun ce tana iya bukatar sahihin matsayar Kwamitin na Kasa (NWC) kafin ta dauki mataki.
Babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a Nigeriya tasha fama da rikice-rikicen a baya, musamman rikicin shugabanci tsakanin bangarorin Makarfi da Sheriff a shekarar 2016–2017. A wancan lokacin, sabanin umarni ya jefa jam’iyyar cikin dogayen shari’o’i da kuma kara raunana hadin kanta.
Idan ba a warware matsalar nan ba da gaggawa, rikicin tsakanin Damagum da Anyanwu na iya sake jefa PDP kotu abin da zai iya karkatar da hankalin ta daga damar da ta dauka a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.