Nijeriya na Ƙara kwarjini a idon duniya qarqashin Tinubu – Ministan Labarai

top-news

Ministan Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewa, Nijeriya na qara kwarjini samun tagomashi da kwarjini a idon duniya qarqashin kyakkyawan jagorancin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake bai wa qasar.
Ministan Labaran ya bayyana hakan ne jiya a tattaunawar da ya yi da Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA) a Babban Taron Majalisar Xinkin Duniya da ake gudanarwa a New York dake Amurka, inda ya qara da cewa, Shugaban Nijeriyar ya qara fito da martabar ba wai kawai Nijeriya ita kaxai ba, a’a, har ma da Nahiyar Afrika bakixaya.
“Ziyara ce mai matuqar ban sha’awa da Shugaban Qasar ya gudanar. Ya zo ne ba don Nijeriya kaxai ba, amma har ma da Afrika,” inji shi.
“Tabbas kun gan shi (Shugaba Tinubu) tare da Shugaban Qasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramophosa; kun gan shi da Shugaban Tarayyar Comoros, Shugaba Azali Assoumani, kun gan shi tare da Aaki Hussein na Jordan da Shugaban Qasar Angola, inda dukkanninsu suka kasance a shirye suke wajen ganin Nijeriya ta daidaita a inda ta dace da matsayinta.
“daga dukkan alamu duniya tana sake maraba da Nijeriya izuwa ga martabar da ta dace da ita. Abubuwa da dama suna ta faruwa.
“Ana sa ido kan Nijeriya don ganin ta yi jagoranci tafiyar, kuma Shugaba Tinubu yana jan ragamar a halin yanzu. Don haka a yanzu Nijeriya tana sake zama muhimmiyar qasa a duniya ta hanyar komawa kan matsayinta da aka san ta da shi.”
Daga nan sai Ministan ya bayar da misali da irin yadda Shugaba Tinubu ya gabatar da tsararre kuma kyakkyawan jawabinsa a gaban Babban Zauren Majalisar Xinkin Duniyar, inda ya tabbatar da tsarin siyasar dimukraxiyya a matsayin tsari mafi inganci dake bayar da cikakken ’yanci da jin daxi da walwala ga al’umma da kuma yadda Afrika ke fama da tashe-tashen hankulan masu tsattsauran ra’ayi a nahiyar ta yadda ta janyo hankalin qasashen duniya, don su kawo agaji a yankin.
Daga nan sai Malagi ya yi wa ’yan Nijeriya albishir kan yadda Tinubu ya samu amincewar Kamfanin ExxonMobil, wanda ya yi alqawarin samar da makamashi 40,000 a matsayin sabon zuba jari a qasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *