Katsina Times
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), reshen jihar Katsina, ta bayyana alhinin ta bisa rasuwar Sarkin Ruman Katsina, Hakimin Batsari, inda ta bayyana marigayin a matsayin mutumin da yabada muhimmiyar gudunmawa ga zaman lafiya da ci gaban al’ummarsa.
A cikin sanarwar da shugaban ACF reshen Katsina, Alhaji Shehu Musa Malumfashi, ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce rasuwar Hakimin Batsari babban rashi ne ga iyalansa da ma daukacin al’ummar karamar hukumar Batsari, da jihar Katsina.
Kungiyar ta bayyana cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da shugabanci na gari a karamar hukumar ta Batsari, tare da samar da ci gaba a fannoni daban-daban.
“Kungiyar ACF ta kadu matuka da wannan rashi. Muna mika ta’aziyya ga iyalan marigayin da daukacin mutanen karamar hukumar Batsari. Muna rokon Allah Ya jikansa da rahama, Ya kuma saka masa da aljannar firdausi, Amin,” in ji sanarwar.
Arewa Consultative Forum ta kuma yi addu’ar Allah Ya ba iyalan marigayin da al’ummar Batsari hakuri da juriyar wannan babban rashi.