Shugabar matan tafiyar tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa, Hon. Amina Rumah, tare da wasu fitattun jiga-jigan mata na tafiyar siyasarsa, sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar ADC zuwa APC domin bada gudunmuwa ga nasarar tazarcen Gwamna Malam Dikko Umar Radda a zaben 2027.
Hon. Amina Rumah ta bayyana haka ne bayan wata ganawa da Gwamna Radda, wacce tsohon dan takarar dan majalisar wakilai na tarayya, Hon. Musa Yusuf Gafai, ya jagoranta. Tattaunawar ta kammala ne da sahalewar shugabar matan da magoya bayanta su rungumi tafiyar gwamnan bisa la’akari da ayyukan raya kasa da yake aiwatarwa a sassan jihar Katsina.
“Na bar tafiyar gidan Mustapha Inuwa ne saboda ayyukan alheri da Gwamna Dikko Radda ke yi wa lungu da sako na jihar Katsina. Na ga ya dace mu bada gudunmuwa wajen tabbatar da cigaba da nasarar sa,” in ji Amina Rumah.
Ta kuma tabbatar da cewa matan za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin wayar da kan mata a fadin jihar su sake zabin Malam Dikko Radda a zaben 2027.
Hon. Rumah ta ce babban dalilin da ya janyo wannan sauyi shi ne yadda Dakta Mustapha Inuwa ya yi watsi da matan tafiyarsa duk da kokarin da suka dinga yi tun daga shekarar 2023 a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana wannan sauya sheka a matsayin babban giɓi ga tafiyar Dakta Mustapha Inuwa, tare da bayyana cewa zai iya zama ƙalubale ga tasirinsa a siyasar jihar Katsina a zaben 2027.