Majalisar Kansilolin Mashi A Jihar Katsina Ta Tsige Shugabanta Saboda Rashin Ƙwarewa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29082025_210731_FB_IMG_1756501526855.jpg

...Bishir Musa ya zama sabon Shugaban Majalisar, Haruna Dahiru ya karɓi mukamin babban mai tsawatarwa

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Juma’a, 29 ga Agusta, 2025

Majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Mashi a jihar Katsina ta tsige shugaban majalisar, Hon. Sama’ila Idris, Kansila daga Mazabar unguwar Tamilo A, daga mukaminsa na shugabanci.

An ɗauki wannan mataki ne a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Juma’a, 29 ga watan Agusta, 2025, a dakin taro na sakatariyar ƙaramar hukumar Mashi, da ya samu halartar Kansiloli takwas daga cikin goma shadaya (11) na ƙaramar hukumar. 

Wakilin Jaridar Katsina Times ya ya halarci zaman wanda wanda a cikin sa ne aka bayyana ƙudirin da aka gabatar a gaban majalisar. Sunce an tsige Sama’ila Idris ne bisa rashin ƙwarewa, gazawa wajen gudanar da ayyukan majalisa, da kuma aikata manyan laifuffuka na rashin ɗa’a.

Biyo bayan haka, majalisar ta amince da zaɓen Hon. Bishir Musa, Kansila mai wakiltar unguwar Jigawa, a matsayin sabon shugaban majalisar, yayin da Hon. Haruna Dahiru, daga unguwar Sonkaya, ya karɓi mukamin Babban mai tsawatarwa 

Ƙudirin tsige shugaban ya samu goyon bayan mafi rinjaye daga kansilolin majalisar da suka haɗa da:

1-Hon. Bishir Musa (Jigawa)

2-Hon. Babangida Haruna (Doguru B)

3-Hon. Aminu Isa (Doguru A)

4-Hon. Haruna Dahiru (Sonkaya)

5-Hon. Bara’u Abdu (Gallu)

6-Hon. Sagir Abdullahi (Shuaibu Mashi)

7-Hon. Surajo Tukur (Tamilo B)

8-Hon. Nura Surajo (Karau)

Majalisar ta tabbatar da cewa kwafin ƙudirin an aika shi zuwa Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi na Jihar Katsina, Shugaban Ƙaramar Hukumar Mashi, Shugaban Ma’aikata na Gunduma, DPO na ‘yan sanda a Mashi, ofishin DSS da kuma na NSCDC domin tabbatar da lamarin.

A cikin sanarwar, majalisar ta ce sauyin shugabanci ya zama wajibi domin dawo da nagarta, da tabbatar da wakilci nagari ga jama’ar ƙaramar hukumar Mashi.

Follow Us