Gwamnatin Katsina za ta gudanar da bincike kan Tamowa a jihar.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26082025_192206_FB_IMG_1756236073724.jpg



Gwamnatin Jihar Katsina za ta gudanar bincike na musamman domin gano yadda matsalar rashin abinci mai gina jiki (Tamowa) wato 'malnutrition' a turance, ke shafar al’umma a daukacin kananan hukumomi 34 na jihar.

A yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da aikin binciken, Mukaddashin Gwamnan Jihar, Honorabul Faruq Lawal Jobe wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Tanimu Dutsin-ma ya wakilta ya bayyana cewar, manufar binciken shi ne tantance al'ummomin da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, nazartar raunin karfin Iyali ga cimaka mai gina jiki, da kuma kayyade matsakaicin kudin da ake gashewa a gida don abinci.

Ya ce, gwamnatin jihar ta dauki matakai na dogon lokaci wajen tsaron abinci, ciki har da: Siyan manyan taraktoci 400 domin inganta noma, Samar da taki mai rangwame ga manoma, da ninka tallafin kudade ga harkar noma daga Naira Miliyan 200 a shekarar 2023, zuwa Naira Miliya 250 a shekarar 2024 da kuma lillinka su zuwa Miliyan 500 a shekarar 2025, yana mai cewar "Tun zuwan wannan gwamnatin ta Malam Dikko Radda ake ci gaba da samar da taki mai rangwame ga manoma don samun amfanin gona mai yawa."

A cewar Jobe, wannan bincike da za a aiwatar zai ba gwamnatin damar kara bibiyar ci gaban ayyuka da tantance tasirinsu, domin tabbatar da  kokarin da gwamnatin ke yi ya yi tasiri kuma ya bada fa'ida.

A yayin jawabinsa, shugaban kwamitin, Sheikh Ahmad Filin-Samji, ya bayyana cewar binciken zai ratsa gidaje 8,500 a fadin jihar, tare da horas da kusan ma'aikata 200 domin tattara bayanai bisa ka'idar duniya.

Filin-Samji, ya kuma yi kira ga ma'aikatan da za a horasa fa su dauki aikin a matsayin ibada, tare da sadaukar da kansu domin ci gaban al'umma.

Shi ko a nasa jawabin, Farfesa Saifullahi Sani, babban Jami’in Kididdiga na Jihar Katsina, ya ce tattara sahihan bayanan da za a yi zai taimaka sosan gaske wajen samar da tsare-tsaren rigakafi da kariya kan yunwa da rashin abinci mai gina jiki, domin a magance matsalar tun kafin ta tsananta.

Follow Us