BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA GWAMNATIN JIHAR KATSINA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26082025_175708_FB_IMG_1755963646573.jpg

Akan Hirar da Aka Yi Game da Makarantun Masu Zaman Kansu da ke Ba da Shaidar Diploma da NCE

A ranar 23 ga watan Agusta, 2025 gidan rediyon Vision da ke Katsina ya gudanar da shirin Babbar Magana tare da Farfesa Machika, Farfesa Matazu da Malam Ruwan Godiya, inda aka tattauna kan makarantun al’umma da na masu zaman kansu da ke ba da shaidar Diploma da NCE.

Sai dai abin takaici, mu a matsayin Concerned Citizens, mun lura cewa tattaunawar ba ta yi adalci ba, saboda ta fi karkata wajen rage darajar waɗannan makarantu, tare da yin zargi ba tare da hujjoji masu ƙarfi ba.

A matsayinmu na ‘yan ƙasa da abin ya shafa, muna jin daɗin bayyana hujjojinmu a bayyane domin a samu adalci:

HUJJOJINMU

1. Batun lasisi da rajista
An ce makarantun ba su da inganci kuma ba su da rajista. Amma a gaskiya, kusan dukkan waɗannan makarantu gwamnati ce ta duba ta kuma ba su lasisi a lokacin da jami’an gwamnati ke shugabantar ma’aikatar kula da ilimi mai zurfi. Har ma ana karɓar haraji daga gare su. Idan yanzu ana kiran su marasa inganci, hakan yana nuni da rashin daidaito a matakin farko na bayar da lasisi.

2. Batun takardar shaidar bogi
An yi ikirarin cewa makarantun suna bayar da takardun bogi. Amma gaskiyar ita ce, ɗaliban da suka kammala a makarantu da dama sun ci gaba da karatu a jami’o’i, wasu kuma sun samu ayyuka har ma da mukamai a cikin gwamnati. A aikace, takardar makarantar ba ita ce ta ƙarshe ba, domin akwai mother institutions da ake da alaƙa da su. Haka kuma, korar wasu daga aikin ‘yansanda ba za a iya jingina ta da makarantun ba, domin yawanci ana ɗaukar su ne da SSCE, ba da Diploma ko NCE kai tsaye ba.

3. Batun ƙwarewar malamai
An yi zargin cewa malaman ba su da ƙwarewa. Amma a bincike, kaso mafi girma na malaman da ke koyarwa a waɗannan makarantu malamai ne na gwamnati da ke zuwa don taimakawa al’ummarsu. Wannan ya nuna ba wai babu ƙwarewa ba, illa dai akwai haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma.

4. Batun kuɗin gudanarwa
An ce makarantun ba su da kuɗin gudanarwa. Amma gaskiya ita ce, makarantu na gwamnati da ake ba tallafi ma suna fama da matsalolin gudanarwa. Sai dai makarantun masu zaman kansu sun kasance mafita ga ‘yan kasuwa da iyaye da ba za su iya tura ‘ya’yansu zuwa makarantu na gwamnati ba saboda nisan hanya ko tsadar sufuri.

5. Batun affiliation
An ce an haramta affiliation. Amma a cikin lasisin da gwamnati ta bayar da kanta akwai sharadin neman affiliation daga manyan makarantu. Wannan yana nuna cewa ba haramun aka ce ba, sai dai tsarin da ake bukatar a bi. Idan yanzu an canza matsaya, bai kamata a jingina laifi ga makarantu ba.

6. Batun lalata ɗalibai
An ce makarantu suna ɓata ɗalibai. Wannan magana tana buƙatar hujja mai ƙarfi. A zahiri, iyaye sun shaida irin tasirin da makarantun suka yi wajen tallafa wa ‘ya’yansu, musamman masu ƙaramin hali da ba su da damar zuwa makarantu na gwamnati.

7. Batun arha a makarantu na gwamnati
An yi ikirarin cewa makarantu na gwamnati su ne mafi arha a Najeriya. Amma idan aka kwatanta da wasu jihohi kamar Jigawa da Kano, akwai makarantu masu zaman kansu da ke bayar da kudi ƙasa da na Katsina. Idan ana son tallafa wa talaka, abin da ya fi dacewa shi ne a ba da shawarar rage kuɗin rajista na makarantun gwamnati maimakon a hana al’umma damar samun mafita daga masu zaman kansu.

8. Batun amfani da JAMB
An ce duk makarantar da ba ta amfani da JAMB makarantar banza ce. Amma a zahiri, akwai tsarin continuing education da open universities da ba sa amfani da JAMB kai tsaye, sai dai regularization. Hakan ya nuna cewa hanyar samun ɗalibai ba ta tsaya ga JAMB kadai ba.

KIRANMU GA GWAMNATI

Muna roƙon Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina da ya yi duba da adalci kan wannan al’amari.
Makarantun masu zaman kansu suna taka muhimmiyar rawa wajen ba da damar karatu ga matasa da kuma tallafawa gwamnati wajen rage nauyin da ke kanta.

Rushe su ko rage musu ƙima zai iya haifar da ƙarin matsalar jahilci, zaman banza da ƙara yawan matsalolin tsaro a jihar.
Abin da ya fi dacewa shi ne a inganta tsarin kulawa da su, a duba yadda za a ƙarfafa su su ci gaba da bayar da gudummawa ga ilimin ‘ya’yan talakawa.

A ƙarshe, muna sake jaddada cewa manufarmu ita ce neman adalci da gyara, ba ɓatanci ko cin mutunci ba.
Muna fata gwamnati za ta saurari wannan kira cikin hikima da adalci.

Sa hannu: 
Mannir Dutsin Safe. A madadin Concerned Citizens
08141587890

Follow Us