A yau Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, an gudanar da taron manema labarai domin sanar da shirye-shiryen bikin Ranar Hausa ta Duniya da za a gudanar gobe Talata, 25 ga watan Agusta, 2025 a garin Daura.
Da yake jawabi a lokacin taron, Babban dan jarida kuma wanda ya kafa wannan ranar Hausa ta duniya Alhaji Abdulbaki Aliyu ya bayyana cewa” An shirya wannan taro ne domin bayyana muhimmancin ranar, tare da jawo hankalin al’umma kan irin rawar da harshen Hausa ke takawa wajen bunkasa al’adu, ilimi da kuma hadin kai tsakanin al’ummomi daban-daban a fadin duniya”.
Haka zalika ya bayyana cewa za a gudanar da taron babba a garin Daura a gobe, wanda zai kunshi jawabai daga masana, marubuta, da kungiyoyi masu fafutukar raya Hausa, tare da shirye-shiryen nishadi na al’adu.
Ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan jarida da al’ummar kasa da kasa da su halarci bikin wanda zai gudana a garin Daura domin hada kai wajen girmama da kuma kara bunkasa harshen Hausa, wanda ya kasance daya daga cikin manyan harsunan Afirka da duniya ke ji.