Dauke Ɗaliban Jami'ar Gusau: Gwamnan Zamfara ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro
- Katsina City News
- 22 Sep, 2023
- 679
- AN CETO ƊALIBAI SHIDA TARE DA KASHE ‘YAN BINDIGA DA DAMA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaron Jiha, biyo bayan sace ɗaliban Jami’ar Tarayya dake Gusau.
Wannan taron gaggawan an kira shi ne saboda ɗaliban da aka sace a muhallinsu dake wajen jami’a, a Ƙauyen Sabon Gida na ƙaramar Hukumar Bungudu.
A wata sanarwar manema labarai, wacce mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar yau Juma’a, ta ce an kira taron gaggawan ne domin tabbatar da ganin an ceto dukkanin waɗanda aka sace, tare kuma da bin hanyoyin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar Zamfara.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya ba mataimakinsa Mani Mallam Mummuni umarnin jagorantar taron na majalisar tsaro.
Ya ce: “A yayin wannan taro, shugabannin ɓangarorin tsaron na Zamfara sun tabbatarwa da mataimakin gwamnan ƙudurinsu na wanzar da zaman lafiya. Sun kuma shaidawa mataimakin gwamnan cewa sun samu nasarar ceto mutum Shida cikin waɗanda aka sace.
“Sun ƙara ƙara da cewa, jami’an tsaro sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama cikin waɗanda suka saci ɗaliban, inda kuma suke ci gaba da bin sahun ragowar.
“Mani Mallam Mummuni ya ja hankalin shugabannin tsaron da su ƙara tsananta sintirin jami’an tsaro a wuraren da aka san suna da hatsari.
“Daga ƙarshe mataimakin gwamnan ya jaddada wa al’umman Jihar Zamfara cewa gwamnati da jami’an tsaro ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, har sai an shawo kan wannan matsala.