Hukumar Hisba A Katsina Ta Bayyana Ayyukanta A Matsayin Masu Amfanar Da Rayuwar Al'umma.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21082025_215703_FB_IMG_1755813172787.jpg

Daga Wakilan Mu (Katsina Times/Taskar Labarai)

Dr. Abu Ammar 

Hukumar Hisba Katsina ta bayyana ayyukanta a matsayin masu amfani kuma abin bukatuwar rayuwar al'umma, hatta ga rayuwar masu badala.

Kwamandan Hukumar, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) ne ya bayyana haka a yayin wani taron manema labarai da hukumar ta kira kan "Hukumar Hisba: Tsare-tsare, Ayyuka, da ci gaban da take samu a fadin jihar Katsina" a ranar Alhamis din, wanda jaridun Taskar Labarai da Katsina Times suka halarta.

Dr. Abu Ammar, ya fara bada tarihin asalin samar da hukumar ta Hisba a Katsina, yana mai cewar ta samu ne sakamakon kiraye-kirayen da al'ummar jihar wadanda suka hada da wayayyun 'yan boko, Malamai, Attajira da 'yankasuwa da sauran jiga-jigan jihar suka sha yi ga Shugabannin jihar a baya.

Ya ce sakamakon kara matsa kaimin bukatuwar samar da hukumar ne da al'ummar jihar suka nace yi ne ya sa a lokacin tsohon gwamnan jihar, Aminu Masari, ya kafa kwamitin samar da ita, Majalisa ta yarda, shi kuma ya sanya wa dokar hannu, inda zuwa gwamnatin Malam Dikko Radda ba ta yi wata-wata ba ta kafa ta.

Dr, Aminu Usman ya ci gaba da cewad, a yagin fara shirye-shiryen gudanar da ayyuka .n hukumar bayan da aka ba shi jagorancinta, ya ce ya ziyarci daukacin Malamai na kowane bangare a jihar, tare da Sarakunan Katsina da Daura don neman hadin kai da yin aikin tare, inda suka ba shi goyon baya, inda aka dauko jami'an hukumar daga kowane bangaren Musulmi, domin hukumar ta kowa da kowace.

"Hisba ta jihar Katsina, Hisba ce da ta tattaro kowa. Babu wani bangare na al'umma da ke rayuwa a cikin jihar katsina da bai da wakilci a cikin hukumar Hisba." In ji shi

A cewarsa, bayan fara gudanar da aikace-akace, dokar farko da suka fara ayyanawa daga hukumar ita ce ta hana DJ, wadda ya ce ita ce doka wadda ta fi ba su ciwon kai da wahala daga al'umma fiye da sauran dokoki duba yadda DJ din ya shiga ciki zuciyar matasa sosai.

Daga nan, Sheikh Abu Ammar ya jero sauran dokin da hukumar ta ci gaba da ayyanawa sannu a hankali a jihar don kawar da badala da tabarbarewar tarbiyyar al'umma da suka hada da: Askin banza, Caca, goyon mata uku a kan Babur, hana daukar mata biyu a gaban kurkura da saka kide-kide, zakulo gidajen mata masu zaman kansu da suransu.

Da yake bayyana irin nasarorin da hukumar ta samu tsawon lokacin kafa ta zuwa yanzu, Kwamnadan na Hisba ya bayyana sasancin ma'aurata a matsayin babbar nasara wanda suka jin dadinsa, domin a cewarsa hukumar ta sasanta aure daban-daban har sama dubu shida.

A bangaren gidajen mata masu zaman kansu da 'yanmata masu yawan banza kuwa, ya ce ya zuwa yanzu sun maida sama da mata guda dari biyar zuwa ga iyayensu, a yayin da wasunsu ma hukumar ce ta jagoranci auran da su hadin giwa da gidauniyar Hawwa Radda, kuma hukumar na ci gaba da saka idanu kan auren don tabbatuwarsa.

A bangaren sasancin bashi, rigimar gado da ta Ahali, da canja halayen kangararu, Abu Ammar ya bayyana hakan a matsayin ita ma wata babbar nasara da hukumar ke kan samu, domin ya ce a bangaren sasancin bashi hatta Kiristoci sun sansanta tsakaninsu, kuma kowanensu ya gamsu.

Sheikh Aminu Abu ammar ya karkare da cewar, hukumarsu ta Hisba ba ta shiga ko yin katsalandan a cikin aikin wata hukuma, sai ma dai taya hukumomin aiki, domin ko sun kama masu laifi, to suna hannanta su ne ga hukumar danke da alhakin ji da wannan laifin.

Daga karshe, Abu ammar ya nemi al'ummar jihar da su kara ba su hadin kai da goyon baya don kakkabe bayyannanniyar barna a cikin al'ummar jihar.

"Mu hukumar Hisba ta jihar Katsina muna aiki don Allah don gina ingantacciyar tarbiyya, kuma muna kiyaye hakkokin da Allah ya dora wa dan'adam da abokin zamansa.

"Hukumar Hisba hukuma ce wanda jigon aikinta yana da alaka da tarbiyyar al'umma kaitsaye, ta hanyar umurni da kyakkywa da kuma hana mummuna." Ya nanata

Follow Us