...Da wanene dalili aka kaishi? Suwa suka hadakai
Daga wakilanmu.
A ranar talata 19 ga watan Agusta 2025 'yan fashin daji suka kai wani mummunan hari na rashin imani a garin gidan Mantau dake karamar hukumar Malumfashi.
A harin an kashe sama da masallata ashirin, lokacin suna tsakar sallar asuba an kuma kashe wasu mutanen a cikin garin na Mantau.
Binciken jaridun katsina times ya tabbatar da cewa harin na ramuwar gayya ne ga mutanen garin. Binciken mu ya tabbatar mutanen garin mantau, kansu hade yake wajen kokarin kare garinsu daga duk wani hari na barayin daji.
Binciken mu, ya tabbatar mana sun sha ba 'yan fashin daji kashi wajen fafatawa. Bincikenmu ya tabbatar da cewa barayin daji na tsoron garin.
Binciken mu ya tabbatar wanda ya jagoranci barayin da sukayi wannan ta 'asa shine sanannen dan ta'addar nan dake yankin kankara mai suna Mustapha Babaro, ana zargin cikin tawagar shi wadanda suka kai harin akwai wani barawon mai suna Janduna da wani dan fashin mai suna Isiya kwashengarwa.
Binciken mu ya tabbatar Babaro bai samu nasarar shiga garin mantau ba sai da yayi amfani da sasanci da yayi da mutanen 'yar goje ya kuma nemi hadin kai da rufin asiri na mutanen kauyukan dake kusa da garin na Mantau.
Babaro ana zargin ya fada ma, mutanen kauyukan cewa zaije daukar fansa ne kuma yana son ya shammaci mutanen gidan Mantau.
Binciken mu ya tabbatar da cewa Babaro ya nufi garin Mantau da sama da mashin dari. Ya kuma yada zango a garuruwa uku, harda inda suka sha mai da wani gari da suka tsaya suka tsara harin.
Ana zargin Babaro ya bar inda suka tashi zuwa kai harin kafin dare ya tsala. wanda akwai kyakkyawar dama ta ana iya sanar da jami an tsaro ko kuma a sanar da mutanen garin mantau su shirya.
Binciken da mukayi a wasu garuruwan sun tabbatar mana cewa barayin sun tsorata su da cewa in har suka samu matsala a harin gidan mantau asirin su ya tonu to lallai zasu dawo kansu.
"Wannan ya sanya muka tsora ta mukayi shiru da bakinmu " inji wani da yana fada mana bisa amana.
Binciken mu ya tabbatar da hanyoyin da barayin suka bi suruki ne da lunguna zuwa gidan Mantau wanda koda za a iya kai daukin gaggawa sai dai ta jirgin sama.
Gidan Mantau yana cikin yankin karfi karamar hukumar Malumfashi, jahar katsina.
Mustapha Babaro babban barawo ne da yake da karfi a yankin karamar hukumar kankara, Dan shekaru 30 zuwa talatin da shidda. Ya dade yana harkar sata tun ta kaji da tumaki kafin ya dauki manyan makamai.
Binciken mu ya tabbatar an sha kama shi akan harkar sata a sake shi an kuma taba kama shi akan harkar barawon daji shima ba a san ya ya fito ba.
Ana zargin yana cikin wadanda suka saci janar tsiga, kafin ya samu "yancin bayan an biya kudin fansa.
Binciken mu ya tabbatar Babaro yasha ikirarin sulhu da sasanci daga baya aji shi ya aikata ta'asa