Gyaran Tattalin Arzikin Shugaba Tinubu Ya Baiwa Jihohi Damar Samun Wadatattun Kuɗaden Yin Ayyukan Raya Kasa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20082025_103851_H.E.-Bola-Ahmed-Tinubu-1.webp

Gwamnan Jihar Neja, Malam Mohammed Umaru Bago, ya bayyana cewa manufofi da tsare-tsaren Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun fara haifar da sakamako mai kyau musamman wajen bunkasa tattalin arziki da ayyukan raya kasa a jihar.

Bago ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Arise TV, inda ya ce manufofin gyaran tattalin arzikin gwamnatin tarayya sun baiwa jihohi kasar nan damar aiwatar da manyan ayyuka masu tasiri ga al’umma.

Ya ce, “Shugaban kasa ya kafa tubalin da ake bukata wajen dawo da tattalin arzikin kasa kan turbar ci gaba. Wannan ya ba mu damar bunkasa noma, kiwo, sarrafa ma’adinai da kuma gina muhimman hanyoyi da gadaje a jihar Neja.”

Gwamnan ya jaddada cewa Niger tana da kashi 11% na filayen Najeriya gaba ɗaya, tare da dimbin albarkatun kasa da ake iya sarrafawa don bunkasa tattalin arziki. Ya ce gwamnati ta fara amfani da wannan dama ne bisa ga manufofin Shugaba Tinubu na inganta noma da rage dogaro da man fetur.

“Muna da fiye da kashi 60% na Kadanya a duniya, kuma yanzu muna da masana’antar sarrafa ta a Mokwa. Wannan ya samu ne saboda manufofin gwamnati na kara tallafawa noma da samar da yanayi mai kyau ga zuba jari,” in ji shi.

Haka kuma, Gwamnan ya bayyana cewa shirin gyaran tattalin arziki da Shugaba Tinubu ya jagoranta ya baiwa jihohi karfin karawa ma’aikata albashi da aiwatar da muhimman ayyuka. “Mun kara mafi ƙarancin albashin ma’aikata a Neja zuwa N80,000, mun kuma fara gina sabbin hanyoyi, gadaje da gadoji. Wadannan su ne ainihin sakamakon manufofin shugaban kasa,” in ji shi.

Ya kara da cewa, tsare-tsaren gwamnatin tarayya na habaka noman zamani da kiwo sun dace da yanayin jihar Neja wadda ke da filaye masu yalwa da ruwan sha. “Shirin Livestock and Agricultural Modernization Project (LAMP) zai tabbatar da cewa Neja ta zama cibiyar samar da abinci da nama ga kasar nan,” in ji shi.

Bago ya kammala da cewa, “Idan kana son ganin tasirin manufofin Shugaba Tinubu, ka duba Niger: muna ganin sabbin hanyoyi, sabbin masana’antu, sabbin gonaki da karin ayyukan yi. Wannan shi ne ainihin abin da ake kira canjin tattalin arziki da ci gaban kasa.”

Follow Us