Yan Fansho sama da 90,000 Aka Biya Bashin Da Suke Bi Da Ya Kai Naira Biliyan 5.12 —Gwamnatin Tarayya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12082025_095635_FB_IMG_1754920714051.jpg


Gwamnatin Tarayya ta biya bashin fansho na Naira biliyan 5.12 ga masu ritaya 90,689 da ke ƙarƙashin tsarin Defined Benefit Scheme (DBS) ta hannun Hukumar Pension Transitional Arrangement Directorate (PTAD). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na PTAD, Mista Olugbenga Ajayi, ya fitar a Abuja ranar Litinin, inda ya ce an kammala rabon kuɗin ga dukkan waɗanda zasu amfana.

A cewar Ajayi, masu ritaya daga sassa huɗu na fansho sun amfana da wannan biyan, wanda ke tabbatar da jajircewar gwamnati wajen kula da jin daɗi da walwalar masu ritaya. Masu ritaya daga Sashen Fanshon hukumar Kwastam, hukumar Shige da Fice da Jam’an Gidajen Yari (CIPPD) sun kai mutane 8,626, inda aka biya su N276,032,000 na bashin wata guda. Masu ritaya daga Sashen Fanshon ’Yan Sanda (PPD) kuwa au 9,681 ne, inda suka samu N619,584,000 na bashin watanni biyu.

Haka kuma, masu ritaya daga Sashen Fanshon Ma’aikatan Gwamnati (CSPD) su kama mutane 12,773, inda aka biya su N408,736,000 na bashin wata guda, yayin da masu ritaya daga Sashen Fanshon Hukumomin Gwamnati (PAPD) su ne mafi yawa da adadin su mutum 59,609, inda suka karɓi N3,814,976,000 na bashin watanni biyu.

Ajayi ya ce wannan biyan bashin ya sake tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana tsayawa kan alkawuranta na biyan hakkokin masu ritaya da inganta jin daɗinsu, a ƙarƙashin manufar Renewed Hope Agenda.

Follow Us