Asusun TETFUND Ya Ware Naira Miliyan Dubu 100 Don Bunkasa Ilimin Likitanci a Manyan Makarantu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10082025_193752_d0432-masarii.jpg



Asusun kula da Manyan Makarantu na Kasa (TETFUND) ya saki sama da Naira biliyan 100 ga manyan makarantun kasar nan a matsayin tallafin inganta ilimin likitanci da unguwar zoma da makamantansu domin kara yawan ma’aikatan kiwon lafiya a kasar nan.

Shugaban Asusun na TETFUND, Rt. Hon Aminu Bello Masari, ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Katsina.

Ya ce yin hakan manufa ce ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an shawo kan matsalar karancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya, duba da yadda likitoci da malaman jinya da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya suka yi ta barin kasar nan a 'yan shekarun baya.

“Shugaban kasa ya damu matuka da yadda likitoci da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya suka yi ta barin kasar da kuma yadda lamarin ke shafar bangaren kiwon lafiya, wannan tallafin na cikin kudurorinsa na ganin cewa an cike giɓin da aka samu a wannan fannin.

“An zaɓo manyan makarantu guda uku a kowace shiyya a kasar nan, cikin shiyyoyi shida da muke da su, kowace makaranta za ta samu Naira miliyon dubu huɗu (N4b) don gudanar da ayyuka da zasu kara yawan daliban da za su rika dauka suna horar da su a fannin ilimin likitanci da jinya da ilimin magunguna na zamani da sauransu.

“Manufar ita ce a ruɓanya adadin likitoci da ma’aikatan jinya da masu ilimin hada magunguna a kasar nan, wannan ko shakka babu zai inganta harkar kiwon lafiya a kasar nan.

“Kowace shekara hukumar TETFUND tana aiwatar da ayyuka a matakin jiha da shiyya, don kowane yanki na kasar ya amfana da aiyukan hukumar, bana fannin da aka ba muhimmanci shine fannin ilimin likitanci”, in ji Masari.

Ya yi nuni da cewa asusun yana da tsarin bibiyar aiyukan da ake bayarwa, domin a tabbatar cewa makarantun suna kashe kudaden domin aiyukan da aka ware dominsu.

Tsohon gwamnan kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya ya bayyana cewa a bana hukumar ta TETFUND ta samu mafi girman tallafin da ta taba samu, na Naira tiriliyan 1.6 wanda ya taru daga harajin ilimin da ake cirewa daga ribar da kamfanoni ke samu a kasar nan.

Ya ce ana cire kashi 3 cikin 100 daga ribar kowane kamfani, bisa yadda dokar da ta kafa hukumar TETFUND ta tanadar.

“A cikin wannan adadin, an ware kashi 40 cikin 100, wanda ya kai Naira miliyon dubu 460, domin gudanar da ayyuka daban-daban a manyan makarantun kasar nan.

“A matakin jiha an zabo manyan makarantu uku-uku; da jami'a daya, da kwalejin kimiyya da fasaha daya, da kuma kwalejin ilimi daya, su ne zasu ci gajiyar shirin.

"Ayyukan sun dogara ne akan bukatar da makarantun suka gabatar mana, suna rubuto mana bukatunsu, mu kuma sai mu duba abin da ya fi muhimmanci da kuma kudaden da muke da su a kasa, sai mu amince musu mu sakar musu kudin", in ji shugaban gudanarwan na TETFUND.

Masari ya bayyana cewa, daga cikin Naira Tiriliyan 1.65, an ware Naira Biliyan 225 ga asusun bayar da lamunin ilimi ga dalibai (NELFUND), domin su fara ba dalibai rance a bana.

Ya ce an kuma ware Naira miliyon dubu 70 a matsayin tallafin inganta wutar lantarki a manyan makarantu, ya ce makarantun za su yi amfani da kudaden don hada na’urorin samar da wutar lantarki da hasken rana, wasu kuma da iskar gas.

Shugaban hukumar ta TETFUND ya kuma bayyana cewa hukumar ta samar da Naira miliyon dubu 25 ga wasu manyan makarantu domin su samar da tsaro a makarantun.

“Makarantun za su yi amfani da kudaden ne domin inganta tsaro, wasu zasu sanya fitilun kan titi a harabobinsu da wasu aiyukan daban na samar da tsaro”, in ji Masari.

Follow Us