Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes
Shugabar Ilimin Manya ta Katsina ta jagoranci haɗin gwiwar Arewa don tattauna rage jahilci da inganta ilimi ga marasa galihu
Babbar Daraktar Ilimin Manya (Agency for Mass Education) a Jihar Katsina, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai, ta jagoranci wani gagarumin yunkuri a Arewa don tallafa wa shirin Gwamnatin Tarayya na wayar da kan sama da matasa da manya dubu 500,000 da ba sa makaranta, ta hanyar shigar da su cikin tsarin koyon karatu da sauran shirye-shiryen ilimi na musamman.
An ƙaddamar da wannan shiri ne na gwamnatin tarayya a ranar 30 ga Yuli, 2025, a birnin Abuja, karkashin Hukumar Kasa ta Wayar da Kan Jama’a da Ilimin Manya (NMEC), kuma an tsara shi ne domin kowace cikin jihohi 36 da ke cikin ƙasar. A yankin Arewa maso Yamma, kowace daga cikin jihohin bakwai, Katsina, Kano, Kaduna, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Jigawa ana sa ran za ta gano da kuma ɗaukar aƙalla mutane 646 da za su ci gajiyar shirin, ciki har da ‘yan gudun hijira da yara daga ƙauyuka masu fama da talauci.
Hajiya Kaikai ta bayyana cewa shirin ya fi mai da hankali kan matasa da manya da ke fama da matsalolin rayuwa. “Manufarmu ita ce a samar da daidaitacciyar damar samun ilimi ga kowa da kowa, musamman marasa galihu. Babu wanda ya kamata a bari a baya,” in ji ta.
Domin ƙarfafa nasarar shirin, Kaikai ta jagoranci wata tawaga daga Katsina, Kaduna da Zamfara zuwa ofishin Mashawarciya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Ahamed Tinubu kan shirin ciyar da ɗalibai, Dr. Yetunde Adeniji. Sun tattauna ne kan yadda za a haɗa tsarin ciyar da ɗalibai da shirin ilimin manya don ƙarfafa shiga da ɗorewar ɗalibai a makaranta.
“Mun yi imanin cewa tallafin abinci zai taimaka matuƙa wajen jawo hankalin masu karatu su shiga shirin, kuma su ci gaba har zuwa ƙarewar sa,” in ji Kaikai.
A wani bangare na ƙarfafa ci gaba bayan kammala tattaunawar, Kaikai ta gana da kamfanin Swiftlink wanda tsohon babban jami’in banki, Alhaji Abdulmutallib ke jagoranta, domin samar da horon sana’o’i da ƙarfafa tattalin arzikin masu kammala karatun daga shirin.
Wannan shiri yana cikin manhajar gwamnatin Katsina ƙarƙashin Gwamna Dikko Umar Radda da kuma Gwamnatin Tarayya wajen yakar jahilci da faɗaɗa damar samun ilimi a Arewacin Najeriya.
Hotunan taron ƙaddamarwar da aka gudanar a Abuja: Hajiya Bilkisu Kaikai tare da manyan jami’an da sauran abokan haɗin gwiwa, lamarin da ya nuna cikakken goyon baya da haɗin kai don kawo ƙarshen ƙarancin ilimi a ƙasar.