Wakilinmu na Katsina Times | 30 Yuli, 2025
A wani mataki na tallafawa manoma da kuma habaka harkar noma a mazabarsa, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rimi, Charanci da Batagarawa, Arc. Usman Murtala Banye, ya kaddamar da rabon takin zamani Tirela tara ga manoma a wadannan yankuna.
Taron kaddamarwar, wanda ya gudana a gidan sa dake Katsina, ya samu halartar shugabannin siyasa, masu ruwa da tsaki da manoma daga yankunan kananan hukumomin uku, inda aka bayyana cewa wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren dan majalisar na yaki da talauci da kuma bunkasa arzikin manoma.
Yayin jawabin sa a wajen taron, Arc. Banye ya bayyana cewa a bara sun raba Tirela uku na taki, amma a bana, da taimakon Allah da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, sun samu nasarar samar da Tirela tara domin rabawa manoma. Ya ce takin ya hada da nau’ikan zamani kamar UREA da NPK wadanda ke da matukar amfani wajen kara karfin kasa da amfanin gona.
“Aiki ba kawai na raba taki bane. Mun kuduri aniyar tallafawa manoma da rage musu radadin rayuwa. Noma shi ne ginshikin tattalin arzikimu, kuma dole ne mu zuba jari a ciki domin ciyar da jama’a gaba,” inji shi.
Dan majalisar ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da kawo tsare-tsare da shirye-shiryen da za su kai ci gaba kai tsaye ga al’umma, musamman a fannin noma, lafiya, ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce zai ci gaba da amfani da duk wata kafa da zai iya don ganin an saukaka rayuwar jama’a a mazabarsa.
Arc. Banye ya kuma bukaci shugabannin gargajiya da na siyasa da su tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon tallafin, tare da tabbatar da cewa an bai wa wadanda suka fi cancanta damar amfana. “Mu ji tsoron Allah, mu tabbatar da wannan tallafi ya kai hannun manoma na gaskiya. Wannan shi ne kadai hanyar da za ta kawo mana ci gaba da amincewa,” in ji shi.
Taron ya samu halartar fitattun shugabanni daga kowanne yanki na mazabar, da suka hada da Hon. Yahaya Lawal Kawo daga Batagarawa, Muhammad Ali daga Rimi da kuma Aminu Hassan wanda ya wakilci shugaban karamar hukumar Charanci.
Wannan rabon na daga cikin mafi girma da aka taba yi a yankin, kuma ana sa ran cewa manoma da dama za su amfana da shi a wannan daminar noma, duba da yadda farashin taki ke kara tashi a kasuwa. Haka zalika Danmajalisar ya tanadi dusa, gishiri da sauran magungunan dabbobi don raba wa makiyaya a lungu da sako na kananan hukumomin guda uku da yake wakilta.