GWAMNAN ZAMFARA YA YI TA'AZIYYAR SARKIN KATSINAN GUSAU

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes25072025_141600_IMG-20250725-WA0156.jpg


Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya taya al'ummar jihar juyayin rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello.

Allah ya yi wa Sarkin rasuwa ne yau da safen nan a Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya, yana mai kimanin shekaru 71.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa Gwamna Lawal nuna wannan rasuwa a matsayi wani rashi da ya shafe shi kai tsaye. Yana mai siffata Sarkin a matsayin wanda ya gudanar rayuwar sa wajen ganin rayuwar al'ummar jihar Zamfara ta inganta. 

Gwamna Dauda Lawal ya ce, "Na samu mummunan labarin rasuwar Baban mu, mai Alfarma Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello.
 
"Ina miƙa matuƙar ta'aziyya ta ga majalisar Sarakunan Zamfara, iyalan Sarki, Masarautar Gusau, tare da ɗaukacin al'ummar jihar Zamfara.
 
"Rasuwar Sarkin Zamfara babban rashi ne ga al'ummar jihar Zamfara, Arewa da ma ƙasar nan baki ɗaya.

"Sarkin ya sadaukar da rayuwar sa a shekarun nan 10 da ya ya yi hana mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15, wanda ya hau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015. Ya yi mulki cikin jajircewa da sadaukarwa.

"Marigayin, kafin ya zama Sarki, ƙwararren ma'aikacin gwamnati ne, wanda har sai da ya kai matsayin Babban Sakatare a gwamnatin tsohuwar jihar Sakkwato da ta Zamfara.

"Na rasa murshidin Uba mai basira, wanda ke nuna mani hanya, tare da sauran shugabanni a jiha. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuran sa, ya sa aljanna ce ce makoma.

Follow Us