Katsina Times – 22 ga Yuli, 2025
Bayan kwanaki biyu yana jinya sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Katsina zuwa Daura, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya samu cikakkiyar lafiya, inda ya koma bakin aikinsa a hukumance.
Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar sun tabbatar da cewa an sallami gwamnan daga asibiti, bayan da likitansa ya tabbatar da cewa ya warke ƙwarai da gaske kuma ya shirya don komawa ayyukan mulki.
Gwamna Radda ya bayyana godiyarsa ga al’ummar jihar Katsina da ma ’yan Najeriya baki ɗaya bisa addu’o’i, sakonnin fatan alheri da goyon bayan da suka nuna masa yayin da yake jinya.
“Ina matuƙar godiya da wannan ƙauna da addu’o’in da kuka yi min. Wannan goyon baya zai ƙara min ƙarfin guiwa da sadaukarwa wajen yi wa al’umma aiki,” in ji Gwamnan.
Yayin da ya koma bakin aiki, Gwamna Radda ya sake nanata aniyarsa ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen gwamnatin “Gina Makomar Ka”, wanda ke da nufin kawo cigaba mai ɗorewa da walwala ga jihar Katsina.