Gwamna Lawal Ya Buƙaci Sabbin Alƙalan Zamfara Da Aka Naɗa Su Riƙa Gaggauta Tabbatar Da Adalci

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20072025_175121_FB_IMG_1753033829294.jpg

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci alƙalai da su ba da fifiko wajen gaggauta yanke hukuncin adalci ga al’umma.

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin alƙalan manyan kotuna da kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a da aka naɗa a babban ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa babban alƙalin jihar ce ta rantsar da alƙalan manyan kotuna uku da alƙalan kotun ɗaukaka ƙara uku.

Sanarwar ta ƙara da cewa, alƙalan babbar kotun da aka naɗa su ne Mai Shari'a Garba Sirajo, Mai Shari'a Bashir Rabi da Mai Shari'a Abdullahi Nasir, yayin da alƙalin kotun ɗaukaka ƙarar da aka naɗa su ne Mai Shari'a Ibrahim Jibril, Mai Shari'a Muhammad Sanusi Magami, da Mai Shari'a Sha’aban Mansir.

A nasa jawabin a wajen bikin, gwamna Lawal ya bayyana cewa an naɗa alƙalan ne bayan nazari da kuma amincewar majalisar shari’a ta Ƙasa.

“Zan fara da taya ku murna bisa wannan muƙamai da ku ka cancanta, naɗin da aka yi muku ya nuna kwarin gwiwa da tsarin shari’a ya amince da ku, don haka ina kira gare ku da ku tabbatar da wannan kwarin gwiwa ta hanyar nuna ƙwazo, gaskiya, riƙon amana, da rashin son kai a ayyukanku.

“Ina jinjina wa irin ƙoƙari da jajircewar Alƙalin Alƙalai kuma Shugabar Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Zamfara, Mai shari’a Kulu Aliyu OFR, da kuma ɗaukacin tawagarta, na yin aiki mai kyau, domin duk waɗanda aka miƙawa majalisar shari’a ta ƙasa an karbe su kuma aka naɗa su.

“Tabbas wani muhimmin tubalin gina al’umma mai adalci, shi ne rashin son zuciya da kuma tabbatar da adalci a kan lokaci, wannan magana ta fi dacewa musamman ga gwamnatinmu, yayin da muke ƙoƙarin sauya salon tafiyar da al’amuranmu, mu ƙwato jihar Zamfara, da sake gina al’ummarmu tare da duk wani ɗan ƙasa da zai taka rawar gani.

“Wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga bangaren shari’a na jiha don tallafa wa ƙoƙarin gwamnati mai ci na inganta rayuwar ‘yan ƙasa, ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin bangaren zartarwa da na bangaren shari’a na da matuƙar muhimmanci wajen cimma burinmu. Ina mai tabbatar muku da ci gaba da goyon bayana, kuma gwamnatina za ta samar da fa’idojin da suka dace, alawus-alawus, da kuma yanayin aiki da ya dace don taimaka muku wajen gudanar da ayyukanku.

Gwamna Lawal ya kuma jaddada cewa naɗin alƙalan yana ƙara ƙarfafa ƙwarewar da suke da ita wajen yin hidima domin amfanin al’umma.

“Ba wani hidima ne mai nauyi ba, amma da taimakon Allah za ku yi abin da ya dace. Ya kamata ku ba da fifiko ga adalci wajen sake gina al’umma da maido da amana a harkokin mulki. Gwamnati ta zuba jari a bangaren tsaro, samar da ababen more rayuwa, da kiwon lafiya, da ilimi, da jarin bil’adama a cikin shekaru biyu da suka gabata duk da ƙalubalen tsaro da yankin ke fuskanta.

“Mun ƙara mafi ƙarancin albashi daga N7,000 zuwa N70,000, mun samar da alawus-alawus na Ramadan da Sallah, mun bullo da garabasar ƙarin albashin wata guda da ake kira 'albashin watan 13', mun warware garatuti na shekaru 13 da ba a biya ba daga 2011 zuwa 2023. Mun himmatu wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar Zamfara.

Follow Us