RA'AYIN JARIDUN KATSINA TIMES: Sojoji A Kwamandojin Rundunar Tsaron Al'umma (CWC) ....Wannan Haɗin Bai Yi Ba.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03072025_181526_FB_IMG_1731174780453.jpg


Mulki wahalar sha'ani gare shi. Shugaba kamar wani fursuna ne, sai bayanan da aka gabatar masa. Wani lokaci yakan zama kamar "Robot", sai yadda aka ɗora shi.

Wannan ya sa magabata masu hikima sukan ce, in shugaba ya killace kansa da masu basira ya kammala kashi 65 na nasarar  mulkinsa,wani lokaci mai mulki abin a tausaya masa ne.

A cikin makon nan ne majalisar dokokin jihar Katsina ta tantance mutane uku a matsayin kwamandojin da za su kula da ayyukan jami'an tsaron al'umma da gwamnatin Katsina ta kafa waɗanda ake wa laƙabi da "Katsina Community Watch Corps" (KTCWC).

A ra'ayin jaridun KATSINA TIMES, babban kuskure ne, kuma mai illar gaske wannan runduna mai amfani a ɗauko duk tsaffin sojoji a ba su aikin kula da ita.

Harkar tsaro da Ilminta faɗi gare shi, kuma kowane ɓangare yana zaman kansa ne, ba mai tafiya sai tare da ɗan'uwansa, kuma kowane zaman kansa yake. 

Soja, ɗaya ne daga cikin ɓangarori daban-daban, kuma masu yawa na tsaro. 

Soja shi kaɗai ba zai iya warware matsalar tsaro ba.

Sassan jami'an tsaron nan suna da kishi da kuma gasa a tsakaninsu, fifita ɗaya, yana iya haifar da naƙasu a kan wani, kuma aikin zai iya yin tafiyar hawauniya, ko kuma ya ƙara tsada.

Matsalar 'yan fashin daji, ba matsalar soja ba ce zalla, matsala ce da ake buƙatar tara duk ilmin tsaro a waje ɗaya a inuwa ɗaya a yi aiki tare, kuma a yi don Allah.

Waɗannan kwamandojin da aka tantance, kamata ya yi a ce cikin su akwai tsohon soja da tsohon m'aikacin DSS da kuma  ko tsohon m'aikacin NIA da kuma tsohon jami'in ɗan sanda.

Waɗannan huɗun kowane ilminsa zaman kansa yake, haka ma ƙwarewarsa.

A harkar tsaro ta gaske da gaske soja ana sanyo shi ne daga ƙarshe don aiwatar da kammala aiki a lokacin da buƙatarsu ce kawai ya taso.

Janarori biyu da Laftar Kanal ɗaya? Haba sai ka ce dokar ta-ɓaci a lokacin mulkin soja?

Halin da ake ciki na matsalar tsaron al'umma ce ba yaƙin ƙasa da ƙasa ba.

Duk Nijeriya ba jihar da Allah ya yi mata baiwa da tsaffin ƙwarrarrun jami'an tsaro kamar Katsina. Waɗanda suka samu lambar yabo a lokacin aikin su, ya kamata a ce an gano su an tuntuɓe su, kuma da yawa suna nan ba su kai kansu ba ne, amma jira suke a ce ku taho ku ba da taku gudunmuwar.

Wasun su ba abin da suka rasa na duniya, abin da kawai suke nema gamawa da duniya lafiya.

Daga ɗan abun da jaridun KATSINA TIMES suka sani, matsalar tsaron nan ko dai a yi mata shirin kanta, ko kuma ta ɗau lokaci tana cin kuɗi da rayuka.

Ya kamata mu yi koyi da marigayi Umaru Musa 'Yar'adua wajen ɗauko mutanen da za su yi wa jiha aiki. In an san ka cancanta nemo ka ake a kan ƙwarewarka. Misali yadda ya ɗauko Nasiru Abdul yana aiki Abuja ya ba shi mai ba shi shawara a kan harkar watsa labarai. Ya ɗauko Ahmad Abdulƙadir ya ba shi shugaban gidan talabijin na jihar Katsina,  a lokacin duk bai san su ba, ba su san shi ba. Haka ya kamata a yi wa tsaron jihar Katsina.

Idan zai yiwu a canza fasalin janarorin nan a surka da tsaffin 'yan sanda da kuma tsaffin jami'an DSS ko na NIA.

A tsarin tsaron al'umma wanda shi ne halin da ake ciki da ɓarayin daji, soja shi kaɗai sai dai ya dagula lamarin, a ƙara tsawon lokacin da yawan kuɗin da za a kashe.
Tsari na nasara a fagen daga kamar wasan kwallon kafa ne, kowa akwai inda zai tsaya da lambar da zai buga.
Kamar yakin neman zabe ne, kowa da irin aikin shi da kuma gudummuwar shi.
Kamar tuka abin hawa ne, kowace na'ura na da aikin ta.
Allah ya kawo mana tsaro a jahar mu da kasarmu baki daya.

Katsina times 
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar Taskar labarai 
@ www.taskarlabarai.com 
The links news 
@ www.thelinksnews.com
All on All social media handles 
07043777779.

Follow Us