Auwal ISAH Musa | Katsina Times
Makarantar Koyon Sana'a Ta Katsina, wato Katsina Youth Craft Village (KYCV) a turance, ta yaye dalibai 634 na shekarar 2025.
Taron bikin yayen daliban an gudanar da shi ne a filin wasa na Muhammadu Dikko a ranar Laraba 2 ga Yuli, 2025, tare da damka wa kowane dalibi tallafin kayayyakin irin sana'ar da ya koya daga makarantar kyauta.
Shugaban makarantar, Injiya Abdullahi Kabir Kofar Soro, a jawabinsa, ya bayyana irin kwazon da daliban suka nuna a yayin koyar da su, inda ya tabbatar da cewar kwararrin dailbai ne suka yaye ba rubabi-rubabi ba.
Ya ce, a daukacin fannonin sana'o'in da aka koyar da daliban ( ya bada misalin bangaren Walda da Kanikanci), ya bayyana cewar kusan daukacin Kujeru, Bencina da makamantansu da ake yi a daukacin makarantun gwamnati a fadin jihar, daliban ne ke yin su. Hakazalika a bangaren Kanikanci, nan ma ya bayyana cewar yawancin Motoci da ababen hawan Ma'aikatun gwamnatin jihar, daliban ne ke aiwatar da gyaransu.
Injiniya Kabir, ya kuma gode wa gwamnatin Malam Dikko Radda bisa ga yadda yake ba wa makarantar muhimmanci, har ma ya bayyana irin makudan kudaden da gwamnan ya ware wa makarantar aka siyo kayan sana'o'in da aka damka wa daliban kyauta don ci gaba da sana'o'in da suka koya a matsayin na dogaro da kansau.
Shi ko a nasa jawabin, gwamnan jihar, Malama Dikko Umaru Radda ya jinjinawa hukumar gudanarwar makarantar bisa ga jajircewarsu wajen koyar da daliban yadda ya kamata, tun da har ma ga shi sun kai matakin kwarewa da gogewa.
Gwamna Radda ya kuma kara jaddada shirin gwamnatinsa na tallafa wa matasan jihar domin gyaruwar gobensu ta hanyar samar masu hanyoyin dogaro da kai.
Har wayau, Gwamnan ya kuma sha alwashin kara daga darajar makarantar da bunkasa ta, tayadda a cewarsa, ba a fadin jiha ko kasa ba, duk dalibin da ya kammala makarantar zai iya samun aiki da shaidar kammala makarantar sahoda ingancinta.
Har wayau, Gwamnan ya bayyana cewar za a kara adadin gurabun daliban makarantar, domin kara ba wa matasa da yawa damar shigowa don su amfana Sana'o'in da ake koyarwa kyauta.
Daliban da makarantar ta KYCV ta yaye, sun fito daga tsangar horar da sana'a'i (department) daban-daban da suka hada: Gayran Lantarki, Walda, Kwamfuta, Gyaran gashi, Dinki, Kafinta, Gyaran waya da sauransu.
Taron yayen dalibai ya samu halartar jami'an gwamnati a bangaren gudanarwa da zartaswa na jihar, sarakunan gargajiya, Iyayen dalibai, shugabannin kungiyoyi, tsaffin shugabannin Siyasa da 'yantakara irinsu tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema da Dr. Bugaje da sauransu.