Gwamnatin Katsina Ta Karɓi Bakuncin Taron Daga Darajar Mata a Arewa maso Yammacin Najeriya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02072025_180419_FB_IMG_1751479337597.jpg

Maryam Jamilu Gambo | Katsina Times, 2 ga Yuli, 2025



Jihar Katsina ta karɓi bakuncin taron manyan jami’ai da shugabanni daga sassan Arewa maso Yammacin Najeriya da wasu jihohin kasar, domin ƙarfafa shirin Nigeria for Women Project (NFWP) Wani shirin gwamnatin tarayya da ke nufin inganta walwalar tattalin arzikin mata ta hanyar haɗin gwiwar jihohi.

An gudanar da taron mai taken “Ƙarfafa Mata: Haɓaka Damar Tattalin Arziki da Samun Aiki ga Mata ta Hanyar Haɗin Gwiwar Yanki,” a dakin taro na Banquet Hall da ke gidan gwamnati a Katsina ranar Laraba 2 ga watan Yuni 2025, wanda ya jawo hankalin wakilan jihohin Kaduna, Kano, Jigawa, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Neja da Ogun, tare da wakilai daga Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi ta Tarayya, da kuma Babban Wakilin Bankin Duniya a Najeriya, wanda Mr. Mackell ya wakilta.

Haka kuma, taron ya samu halartar kwamishinonin harkokin mata, shugabannin hukumomi, da jami’an da ke jagorantar shirin NFWP daga jihohin da suka amfana.

A jawabinsa, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana cikakken kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa mata ta hanyar saka jari da sauya manufofi na ci gaba.

Ya bayyana cewa sama da mata 33,000 daga kananan hukumomi uku a jihar Katsina na amfana da shirin NFWP, tare da alkawarin samar da daidaitaccen kuɗi daga gwamnati domin ci gaba da fadada shirin.

“Wannan taro ba kawai ganawa ba ce, illa mu bayyana kudurinmu na tabbatar da cewa mata su ne ginshikin ci gaban al’umma,” in ji Gwamna Radda. “Dole ne mu gina tsarin da zai ba mata damar habɓaka, shugabanci, da sauya al’umma.”

Ya kuma yi kira ga sauran jihohi da su dauki matakan aiwatar da tsare-tsare na zahiri da za su tabbatar da dorewar shirin, musamman ta hanyar horarwa, samun rance, haɗin gwiwa da ƙungiyoyi da cibiyoyin kuɗi.

Ministar Harkokin Mata ta Tarayya, Hajiya Imaan Suleiman-Ibrahim, ta yabawa gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma bisa yadda suke baiwa batun mata muhimmanci.

A cewarta, gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar Bankin Duniya za ta faɗaɗa shirin NFWP zuwa jihohi 32 inda mata miliyan 4.5 za su amfana da saka hannun jari na dala miliyan 540.

“Wannan ba tallafi ba ne kawai; wani muhimmin jarin kasa ne da za ya haifar da ainihin sauyi,” in ji ta.

Ta jinjina wa Gwamna Radda bisa shugabancin sa na kare hakkin mata, musamman yadda ya ware naira biliyan 1 a 2024 domin yaki da cin zarafin mata da kananan yara (SGBV), da kuma naira biliyan 4 a 2025 domin tallafa wa mata masu neman ci gaba da dogaro da kansu.

Ta bayyana cewa kashi 47% na mazauna Arewa maso Yamma ba su da damar amfani da ayyukan cibiyoyin kuɗi, wanda hakan ke hana mata damar samun ci gaba da ƙarfafa gwiwa.

Ministar ta sanar da wani sabon shiri mai suna Renewed Hope Social Impact and Advancement Project for Women, Children and the Vulnerable, wanda zai jawo jarin masu zaman kansu da gidauniyoyi domin tallafa wa ƙungiyoyin mata da harkokin ƙirƙiro darajar kayayyaki.

A nata jawabin, Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Abubakar Yar’adua, ta yabawa Bankin Duniya da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya bisa irin goyon bayan da suka bayar wajen aiwatar da shirin NFWP.

“Shirin NFWP ya nuna cewa idan aka ba mata dama, suna iya jagoranci da kawo ci gaba na hakika,” in ji ta.

Ta jaddada bukatar samar da sauki wajen samun jari da horo ga mata a karkara, musamman gajiyayyu, zawarawa da ‘yan gudun hijira. Ta kuma bukaci hadin gwiwa da cibiyoyin kuɗi da manyan masu ruwa da tsaki don samar da mafita mai dorewa.

“Lokaci ya yi da za mu daina magana kan abinda mata ba za su iya ba. Domin a duk lokacin da aka basu dama, mata na tabbatar da nasara,” ta kara da cewa.

Ta yaba wa Gwamna Radda bisa yadda yake mara wa mata baya a fagen shugabanci da ci gaba, tare da jaddada cewa babu wata mata da ya kamata a bari a baya a irin wannan tafiya ta ci gaban kasa.

Taron ya samu halartar fitattun wakilai da suka hada da: Mataimakan Gwamnonin Jigawa da Zamfara. Wakilan Gwamnonin Kaduna, Kano, Kebbi, Sokoto, Neja da Ogun. Wakilan Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi ta Tarayya, Wakilin Bankin Duniya, Mr. Mackell, Kwamishinoni da Shugabannin Hukumo daga jihohin da ke cikin shirin.

Taron ya kammala da jaddadawa daga dukkan mahalarta cewa ba za a iya cimma ci gaban kasa ba tare da baiwa mata cikakkiyar dama ba.

“Wannan kira ne na hadin kai. Muna gina kasa ce wacce kowace mace za ta samu damar rayuwa da girma,” in ji daya daga cikin mahalarta.

Taron ya tabbatar da matsayin Jihar Katsina a sahun gaba na yunkurin canza rayuwar mata a Najeriya, tare da fatan ganin ainihin sauyi a dukkan fannonin tattalin arziki da zamantakewa.

Follow Us