Mai ba gwamnan jihar Katsina shawara na musamman kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa'i Safana ya ummurci jami'ai masu kula da ayyukan ƙananan hukumomi da su kawo mashi takardun shaidar kammala ayyuka na cibiyoyin noma (Agric Mech Centers) da ake ginawa a ƙananan hukumomin su don shirye-shiryen biyan ƴan Kwangilar da suka kammala aikin cikin lokaci.
Haka kuma, sanarwar ta umarci da a kawo cikkakun bayanai akan cibiyoyin da ba a kammala ba tare da dalillan rashin kammalawar. Mai bada Shawarar yace lallai waɗannan bayanai su iso Ofis ɗin shi daga nan zuwa sati mai zuwa ranar Litinin 7 ga wannan wata.
Hon. Safana, ya bayyana mahimmancin miƙa waɗannan takardun shaidar kammala aiki da kuma rahotan matakin da aiki yake ciki don ƙoƙarin shirin biyan aikin.
Bugu da ƙari, ya sanar da duk masu yin ayyukan cewa dole rahoton aikin su ya kasance yana ɗauke cikin muhimman hotunan aiki na cibiyar ta (AMC) domin Injiniyoyi za su ziyarci ayyukan daga hedkwata don tabbatar da kammala shi kafin a biya kuɗin aikin.
Hon. Lawal Rufai Safana