Kungiyar Tsangaya Ta Zamani Ta Kai Ziyarar Ban Girma Ga Gidauniyar Gwagware a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26062025_230026_FB_IMG_1750978714049.jpg


Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES

Kungiyar Modern Tsangaya Development Association, wadda ke da nufin inganta tsarin karatun allo ta zamani, ta kai ziyarar ban girma zuwa babban ofishin Gidauniyar Gwagware da ke Katsina a ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025. Jagorancin tawagar ya kasance karkashin Shugaban Kungiyar, Gwani Masa’udu Rafin Dadi tare da Sakatare na Jihar Katsina, Malam Dahiru Tijjani Filin Bugu da wasu daga cikin manyan mambobin kungiyar.

An tarbi tawagar ziyarar da karimci daga shugaban gidauniyar, Alhaji Yusuf Ali Musawa. A jawabinsa, Malam Dahiru Tijjani ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce neman hadin gwiwa da tallafin gidauniyar domin ci gaba da kokarin kungiyar wajen gyara da bunkasa tsarin karatun allo. Ya kuma mika takardar da ke kunshe da tsare-tsaren kungiyar da manufofinta ga shugaban gidauniyar.

Tijjani ya bayyana cewa kungiyar ta Modern Tsangaya tana kokarin daidaita tsarin karatun allo ta hanyar hada karatun addini da na zamani da koyon sana’o’in dogaro da kai domin kyautata rayuwar almajirai da inganta makomarsu. Ya nemi tallafi daga gidauniyar domin kara karfi da ci gaba ga ayyukan kungiyar.

Shugaban kungiyar, Gwani Masa’udu Rafin Dadi, a nasa jawabin, ya yaba da yadda gidauniyar Gwagware ke gudanar da ayyukanta cikin tsari da kulawa, musamman wajen taimakawa marasa galihu da kokarin ci gaban al’umma. Ya bukaci da a hada kungiyar Modern Tsangaya cikin shirye-shiryen da gidauniyar ke aiwatarwa a fadin jihar Katsina.

Da yake mayar da martani, shugaban gidauniyar Gwagware, Alhaji Yusuf Ali Musawa, ya nuna farin cikinsa da ziyarar tare da yabawa kungiyar bisa kishinta da jajircewa wajen kawo sauyi ga tsarin karatun allo. Ya bayyana cewa, daya daga cikin dalilan kafa gidauniyar shi ne domin yin aiki tare da kungiyoyin al’umma da malamai kamar su.

Alhaji Musawa ya sha alwashin hada kai da kungiyar Modern Tsangaya, inda nan take ya bayar da umarni a shigar da su cikin wani shiri na karfafa kungiyoyin al’umma da gwamnatin jihar Katsina ta amince da shi. Baya ga haka, ya yi alkawarin tallafa wa kungiyar da kayan aiki da sauran ababen bukata don inganta ayyukanta, tare da yin wata ganawa ta musamman da shugabannin kungiyar domin tsara hanyoyin aiki tare na dogon lokaci.

Taron wanda aka gudanar a ofishin gidauniyar ya samu halartar manyan mambobin kungiyar daga sassa daban-daban, la’akari da cewa kungiyar tana da wakilci a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar Katsina. Wannan ziyara ta kasance wata babbar dama wajen kara hada kai tsakanin kungiyoyin al’umma da gidauniyoyi masu zaman kansu don bunkasa ilimi da walwalar al’umma a jihar.

Follow Us