Zaharaddee Ishaq Abubakar | Katsina TIMES
Yarmaiwa, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina – Alhamis, 26 ga Yuni, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina tare da hadin gwiwar Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da wasu kungiyoyin ci gaban Al'umma, ta kaddamar da asibitin kula da lafiya na farko (primary healthcare) da aka gyara a unguwar Yarmaiwa da ke karamar hukumar Batsari. Wannan aiki na daga cikin ayyuka 26 da ake kira "Quick Impact Projects" (QIPs) da aka gudanar a karkashin shirin EU na sasanta rikici da farfado da al'umma (Conflict Mitigation and Community Reconciliation Project – CMCRP), domin dawo da zaman lafiya da inganta rayuwar al’umma da rikici ya shafa.
Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda a wajen bikin, ya bayyana aikin a matsayin “tutar fata, hadin kai da cigaba.” Ya jinjinawa EU, Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira ta Duniya (IOM), Mercy Corps, da Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba (CDD) saboda rawar da suka taka wajen aiwatar da shirin.
“Wadannan ayyuka 26 da aka gudanar a Batsari, Kankara, Jibia da Musawa ba gwamnati ko masu tallafi suka aiwatar dasu don kansu ba ba, al’ummomin da abin ya shafa ne suka zaba ta hanyar tattaunawa da tsara aiki tare,” in ji Faskari.
Ya kara da cewa asibitin da aka gyara, wanda ke samun wutar lantarki ta hasken rana, zai ba da kulawar lafiya, tsaftataccen ruwan sha da kuma kula da lafiyar dabbobi. “A yau ba kawai muna kaddamar da wani gini ba ne, muna kaddamar da wani tsari da zai karfafa gwiwar al’umma, daidaita harkokin mulki na yankunanmu, tare da gina tubalin zaman lafiya a jihar Katsina,” in ji shi.
Malam Musa Abdullahi daga Hukumar Kula da 'Yangudun Hijira ta Duniya (IOM), ya bayyana cewa shirin na daga cikin kokarin farfado da yankunan da rikice-rikice suka shafa a arewa maso yammacin Najeriya.
“Shirin yana da manyan manufofi guda biyu: na farko shi ne inganta zaman lafiya ta hanyar karfafa gwiwar al’umma wajen warware rikice-rikice; na biyu kuma shi ne karfafa tsarin shugabanci da hadin kai,” in ji Musa.
Ya bayyana cewa an kafa dandalin tattaunawa tsakanin al’umma (Community Reconciliation Networks – CRNs) da tsarin gaggawa na dakile rikici (Early Warning and Response Systems) don hana barkewar rikice-rikice. Haka zalika, an horar da matasa, mata, shugabannin gargajiya, manoma, makiyaya, da ma’aikatan gwamnati kan dabarun sasanci da zaman lafiya.
“Wannan asibiti da muka gyara, tare da samar da ruwa ta hanyar hasken rana, zai taimaka wajen biyan bukatun al’umma da dabbobi, a matsayin wani bangare na tallafin da muke bayarwa ga gwamnatin jihar da kananan hukumomi,” in ji shi.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnatin Katsina kuma shugaban kwamitin aiwatar da aikin (PSC), Alhaji Mukhtar Saulawa, ya godewa EU saboda amincewa da kara wa’adin shirin da watanni shida bayan jinkirin fara aiki. Ya ce sabon zagayen aikin ya samu amincewa kuma za a fara a watan Yuli, inda dukkan kananan hukumomi takwas da ke sahun gaba a jihar za su ci gajiyar shirin.
“Ina rokon al’ummomin da suka ci gajiyar wadannan ayyuka da su kula da su yadda ya kamata. Kwamitin Raya Al’umma karkashin Dr. Kamal zai taka muhimmiyar rawa wajen dorewar ayyukan,” in ji Saulawa.
Daga cikin manyan baki da suka halarci bikin akwai: Mataimakin Gwamna na musamman kan tallafawa wadanda Ibtila'in 'yan bindiga ya shafa Sa'id Ibrahim Kogunan Jibia, mai ba da shawara kan kiwo da filayen kiwo Yusuf Suleman Jibiya, da Shugaban Karamar Hukumar Batsari da sauran shugabannin al’umma.
Wannan kaddamarwa na daga cikin muhimman matakan da gwamnatin jihar ke dauka domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankunan da rikici ya shafa.